An sami barkewar mumunar tarzoma da safiyar yau a jihar Imo a lokacin zaben fid da gwani na Gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC. Majiyarmu ta shaida mana cewa rikicin ya kaure ne bayan magoya bayan dan takara da Gwamna Rochas Okorocha ya tsayar Mr. Uche Nwosu wanda dan surukinsa ne da matasan garin Amaike suka gwabza fada da ya kai ga kone konen motocin. Su dai matasan gari Amaike sun zargi Gwamna Rochas da dora masu wanda basu so.



Hakazalika matasan sun kone ofishin Mr. Uche Nwosu da ke wajen Makarantar Pramare na Amaike a karamar hukumar Mbaitoli

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://ift.tt/2NYxOPS Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top