Hukumar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta kama wadansu ma’aurata bisa zargin jinginar da dansu dan shekara biyu a kan Naira dubu 180 don biyan kudin hayar gida a Fatakwal. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, Alhaji Hafiz Inuwa ya bayyana wa manema labarai cewa ma’auratan sun shiga hannu ne bayan da uwar yaron, mai suna Magdalene Bassey ta kawo rahoton faruwar lamarin a ofishinsu, inda take karar mijinta, Mista Daniel Bassey da kitsa aika- aikar jinginar da dansu ba tare da amincewarta ba, kuma ya karbi makudan kudi a madadin yaron.
Kwamishinan ya ce, “A ranar 23 ga Yuli ne uwar yaron mai suna Madam Magdalene Bassey ta shigar da kara a babban ofishin ’yan sanda da ke Kalaba, inda ta yi zargin cewa mijinta Mista Daniel Bassey ya dauki dansu zuwa Fatakwal tare da taimakon wata mata mai suna Mummy. A nan take muka tura jami’anmu, suka je suka kamo wanda ake zargin. A yayin binciken ne kuma mijin ya bayyana duk yadda lamarin ya faru, inda ya tabbatar da cewa matarsa tana cikin badakalar dumu-dumu.”
“Yanzu haka dukan mutanen da ake zargin suna nan tsare a ofishinmu, bisa laifin rashin imani da kuma yunkurin salwantar da rai, kuma da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da su a gaban kotu don fuskantar hukunci,” inji shi. Mahaifin yaron ya sanar da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) cewa, ya mika dansu ne a matsayin jingina, inda ya karbi Naira dubu 180 don biyan kudin hayar gidan da yake zaune.
Ya ce “Zuciya ta debe ni zuwa ga aikata haka ne bayan da wani abokina ya matsa mini a kan wasu kudi da na karba a wajensa Naira dubu 21 a matsayin bashin da na biya kudin haya.
Sai wani abokina ya sanar da ni cewa akwai wata mata da take karbar jinginar yara ta ba da kudi. Sannan ya ce a nan take za a ba ni kudin ba tare da yarjejeniyar sayar da yaron ba. To, daga nan ne na garzaya wajen matar, inda ta ba ni Naira dubu 180 bayan da ta karbi yaron. To bayan haka ne surukata ta zo gidan ta tambaye ni yaron sai na yi mata karyar cewa na tura shi hutu ne wajen wani dan uwana,” inji shi. .
Copyright @aminiya
Post a Comment