Wani kwamiti da kan tsaron cikin gida da harkokin gwamnati da kasar Amurka ta kafa, ya fitar da wani rahoto, wanda ya zayyana mutane 4 da suka zama manyan barayi a kasashen Afrika, da ke aikata manyan badakaloli ta hada hadar kudade ba bisa ka'ida a kasashen turai, musamman a Amurka.


Kwamitin ya fara bincike kan hada hadar kudade da Atiku ya ke yi a kasar ta Amurka, tare da fara rubuta wannan rahoton nasa a ranar 4 ga watan Febreru, 2010. Kwamitin ya zayyana badakaloli 5 da Atiku ya aikata na hada hadar kudade a kasar Amurka ba bisa ka'ida ba.

1. Atiku Abubakar ya yi amfani da matarsa ta 4, Jennifer Douglas, yar asalin kasar Amurka, wajen shigar da $40m zuwa cikin kasar Amurka, kudin da ake zargin an sace su ne a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2008. Kudaden sun hada da cin hancin $1.7m daga kamfanin Sieman AG, da ke da matsugunni a Jamus, da juma $38m daga wasu kamfanonin kasashen waje, musamman kamfanin LetsGo Ltd. Inc., Guernsey Trust Company Nigeria Ltd., da kuma Sima Holding Company.

2. Ms. Douglas ta taimakawa Atiku wajen ganin kamfanonin kasashen wajen sun tura kudaden da suka kai akalla $25m a wasu bankuna daban daban na Amurka ta hanyar yanar gizo. Tsawon lokaci bankunan Amurkan basu san daga ina Douglas ke samo wadannan makudan kudade da take ajiyewa. Ganin bankunan sun fara zarginta, Ms Douglas ta soma bude asusun bankuna da sunayen gidauniya, ciki akwai gidauniyar Gede da ta kafa a 2002, sai kuma ta raba kudin ga jami'ar Amurka a Nigeria (AUN) da Atiku ya kafa a 2003, da sauran wasu kungiyoyin taimakon al'umma da ta kafa a kasashe daban daban, duk don boye kudaden.

3. Lauyan Ms. Douglas, Mr Abubakar da kuma jami'ar Azuzn a Amurka, Mr. Weidenfeld ya yi rawa ya yi tsaki akan wani bincike da bankunan Amurka suka soma yi kan $14m da wasu boyayyun kamfanoni suka tura da sunan jami'ar AUN. Ya ce Atiku na turo kudin ne don biyan kudaden hakkokin ma'aikatan jami'ar da kuma harajin kasar Amurka da sauran bukatu.

4. A 'yan shekarunnan, bincike ya fara tsananta kan hanyoyin da Atiku ke samun wadannan makudan kudade. Sanin kowa ne ya shafe shekaru 20 a hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), kuma ya yi aiki a kamfanoni masu zaman kansu na tsawon shekaru 10, kafin daga bisani ya zama mataimakin shugaban kasar Nigeria daga 1999 zuwa 2007. A lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa, Atiku ne ake zargi da kwashe kudi daga gidauniyar fasahar man fetur ta kasa NPTD.


5. A watan Disambar 2008, hukumar tsaro da canjin kudi ta Amurka, ta zargi waji kamfani mai suna Seimens AG, da ke da zama a Jamus, cewar a 2001 da 2002, ya tura akalla $2.8m a matsayin cin hanci ga wasu bankuna da Ms Douglas ta ke da asusun ajiyar kudi a ciki, a cikjn wani yunkuri na baiwa wasu 'yan Nigeria cin hanci. Kamfanin Seimens ya amince da wannan zargi na tura wadannan makudan kudade ta yanar gizo don baiwa kamfanini da jama'a cin hanci, inda ya biya tarar $1.6bn ga kasar Amurka akan aikata wannan laifi.

Sai dai Ms. Douglas ta karyata duk wani zargi da ake mata, amma kwamitin binciken ya bankado wasu bayanan musayar kudade da ke nuni da cewa Ms Douglas ta tura sama da $1.7m daga kamfanin Seimans AG zuwa asusunta na Ms. Douglas da ke Citibank.
Naija.ng.

Post a Comment

 
Top