Shahararen dan wasan Barkwanci Sallau ya mayarda auren amaryarsa Furera da sukai shirin Dadin kowa Arewa24.

Sallau wanda asalin sunansa shine Umar Muh'd Sani Jigirya, ya wallafa hotonsa tareda matar tasa ne a kafar sadarwar Instagram har ya dan yi gajeren rubutu ajikin hoton kamar haka:
Idan baku manta ba a cikin watan August ne Mujallar Fim Hausa Magazine ta wallafa batun rabuwar auren Sallau da Furera bayan sabani da suka samu wanda harta kai ga saki tsakaninsu.

Bayan Sallau ya sanya hoton a Instagram ne mabiyansa sukaita tofa albarkacin bakinsu yayinda wasu ke masa murnanr dawowa da matarsa wasu kuma suna sukarsa dukda basu san dalilinsa na sakin Furera ba. Hausawa ma sunce "Aure rai ne dashi idan lokacinsa yayi saiya mutu".

Ga wanda baisan wacece Furera ba to itace matar Sallau-Kowa-Naka da ya fito a cikin shahararen shirinnan na Dadinkowa wanada ake gabatarwa a gidan telebijin din AREWA24.

Sakin Aure dai yazama ruwan dare acikin jarumai maza da mata dake masana'antar fina finan Hausa,  Saidai abin ba iya kansu ya tsaya abin yama fi kamari cikin alummomi dayawa a Arewacin Nigeria.