Legit hausa
Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar ta yi nasarar kashe Sale Ahmad Sale, babban jami'in watsa labarai na kungiyar Boko Haram tsagin Albarnawi. Tsagin kungiyar Boko Haram da ke karkashin jagorancin Albarnawi na da alaka da kungiyar ta'addanci ta IS da ke gabas ta tsakiya.
Tuni tsagin ya canja suna daga Boko Haram zuwa ISWAP (kungiyar IS reshen nahiyar Afrika ta yamma). Kisan jami'in yada labaran na daga cikin aiyukan dakarun sojin Najeriya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno na kakkabe dukkan manyan jami'an kungiyar Boko Haram.
A sanarwar da hukumar soji ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce tana matukar alfahari da kisan Sale bisa la'akari da irin matsauinsa a tsarin shugabanci na kungiyar Boko Haram, tare da bayyana cewar hakan na nuni da cewar nan ba da dadewa ba zasu kai ga cimma ragowar shugabannin kungiyar Sanarwar ta kara da cewa, kafin a kashe shi, Sale ya jagoranci kai wasu hare-hare da su ka kai ga asarar rayuka a baya.
Kazalika hukumar soji ta bayyana cewar ta yi nasarar gano waye shugaban sabuwar kungiyar JAMA'ATUL NUSRATUL-ISLAMI WAL-MUSLIMINA. Abul-Fadl Iyad Gali, mutumin da hukumar soji ta ce ke jagorantar sabuwar kungiyar. Hukumar soji ta ce zata yi amfani da kayan aikinta na kimiyya domin gano duk inda shugaban kungiyar ya ke tare da dakile aiyukan ta'addanci da su ke ikirarin fara aikatawa a Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
Post a Comment