Hukumar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wadansu samari da ake zargi da aikata luwadi a makabartar Bulukiya da ke Ungwar Dala a birnin Kano.

Wadanda ake zargin sun hada da Ali Yakubu mai shekara 28 da Aminu Garba mai shekara 19, dukansu mazauna Unguwar Dala a birnin Kano.

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya ce jami’ansu ne suka kama matasan a daidai lokacin da suke aikata fasikancin a jikin katangar makabartar.

Dukan wadanda ake zargin sun nuna nadamarsu, inda suka ce tsautsayi ne ya kai su ga aikata laifin.

Sai dai SP Magaji Musa Majiya ya musanta hakan, inda ya ce son zuciya ce ya kai su ga aikata laifin, domin kuwa a kwanaki daya daga cikin wadanda ake zargin Aminu Garba ya fito daga kurkuku a kan aikata irin wannan laifi.

A cewar Majiya, bayan da aka kama wadanda ake zargin an tura su Asibitin kwararru na Murtala don gudanar da bincike kan lafiyarsu. Ya kara da cewa da zarar sun kammala bincike za su tura wadanda ake zargi ga sashe na musamman da ke kula da harkokin cin zarafi da fyade da ke Shahuci kafin a gurfanar da su a gaban shari’a.
Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0

Post a Comment

 
Top