Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya bayyana cewa bazai taba barin kungiyarsa ta Barcelona ba domin komawa wata kungiyar a nahiyar turai saboda babu wata kungiya kamar tasa yanzu a duniya.
Messi ya bayyana hakane a wata hira da yayi da wani gidan radio a kasar Sipaniya inda yace yanzu kungiyoyi da dama sun girma suna iya siyan ‘yan wasan da Barcelona da Real Madrid suke siya saboda haka karfin kowa yakawo.
“Yanzu akwai kungiyoyin da suke da kudade masu yawa kuma ‘yan wasa suna tafiya kungiyoyin saboda kudin saboda haka yanzu komai ya canja karfin Real Madrid da Barcelona na jan hankalin ‘yan wasa ya ragu”
in ji Messi Yaci gaba da cewa “Yana cikin farin ciki a kungiyarsa ta Barcelona kuma baya tunanin barin kungiyar zuwa wata kungiyar a nahiyar turai domin yanada kwantaragi da Barcelona saboda haka sai ya kare sannan zai fara shawarar abinda zaiyi a gaba”
Ya kara da cewa “A lokutan baya kowanne dan wasa yanason ya bugawa Barcelona wasa amma yanzu abin ba haka yake ba kungiyoyi da dama sunada kudi kuma zasu iya kashewa akan duk dan wasan da suke so”
Messi yace akwai lokacin da zaizo dole zai bar Barcelona amma kuma idan yatafi babu wani abu da zai canja a kungiyar idan har shugabannin kungiyar sukaci gaba da rainon matasan yara daga karamar kungiyar sannan kuma suka cigaba da siyan kwararrun ‘yan wasa.
Acikin ‘yan wasan da hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware guda uku da suka hada da Ronaldo da Modric da Salah domin lashe gwarzon dan kwallon duniya babu Messi kuma rabon da a fitar da sunayen babu shi kusan shekaru goma kenan da suka gabata.
Read More at: https://leadershipayau.com/2018/09/06/ba-zan-taba-barin-barcelona-ba-zuwa-wata-kungiyar-a-nahiyar-turai-messi/

Post a Comment