A kalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga jam'iyar APC zuwa PDP a karamar hukumar kuje dake garin Abuja.


Mutanen da suka koma sun sha alwashin baiwa jam'iyar PDP dukkanin goyon bayan datake bukata.

 Shugaban jam'iyar PDP a garin Abuja ya jinijina musa bisa hukuncin dasuka yanke na barin jam'iyar APC tareda komawa jam'iyar PDP. Kuma ya bukace su da su saki jikinsu kasancewar yanzu jam'iyar PDP gida daya ce kuma a gyare. Tare da yi musu alkawarin adalci ba tare da nuna bambanci a tsakaninsu da tsofaffin ya'yan jam'iyar ba.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka sauya shekar shugaban Kwankwasiyya na yankin Alhaji Musa Hassan Shama yace sauya shekar tasu biyo bayan umarnin ubangidan nasu daya bayar cewa duk wani magoya bayansa sukoma jam'iyar PDP. 

Yace abin takaici ne canjin da suka zaba a 2015 bashi suke gani a yau ba, illa ma babban kuskure da suka tafka, yana jawabin cewa da yawan mutane sun tsinci kawunansu a cikin talauci, yunwa, rashin cika alkawarurrukan da jam'iyar APC ta dauka a lokacin kamfen din su na 2015, uwa uba kuma da rashin tsaro ya mamaye kasar a karkashin mulkin jam'iyar APC.
Rariya.

Post a Comment

 
Top