Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa yanzu ba'a yawan ganinta a fina-finai sosai ba kamar shekarun baya ba.

Nafisar tana bayyana hakane a lokacin da take baiwa wani masoyinta amsar tambayar da yayi mata na cewa, yana daga cikin masoyanta kuma fim din tane yafi son kallo fiye da na ko wace jaruma amma me yasa yanzu bata yin fim?

Nafisa ta amsa mai da cewa, na gode da soyayyar da kake min, ina da wasu harkoki da nake gudanarwa akwai matukar wahalar gaske in rika yin fim da kuma kula da sauran ayyukana a lokaci guda, saboda yin fim yana cin lokaci sosai amma idan na samu labari me kyau,nakan yi kokarin yi.

Ta kare da cewa, kayi hakuri a watan Disambar nan zaka ganni a kwalba insha Allah.


Post a Comment

 
Top