Ga sunayen jaruman Kannywood da suka lashe kyautar gasar city people movies Awards na wannan shekarar.


Kamar yadda aka saba a ko wani shekara, an gudanar da bikin karrama a fitattun jarumai da suka taka rawar gani  a harkar nishadi na mujallar City People.

An gudanar da bikin bana a babban wajen taron biki na Balmoral event center dake jihar Legas ranar Lahadi 16 ga watan Satumba.

ga wadanda basu sani ba, bikin City People Movies Awards tana karrama jarumai na dandalin fim na ko wani masa'anta dake fadin kasar.


Bana dai a rukunin yan Kannywood Sadiq Sani Sadiq da Hafsat Idris suka lashe kyautar gwarazan shekara.

Ga sunayen wadanda suka lashe kyautar gasar na rukunin hausa daga masana'antar Kannywood kamar haka:

Sadiq Sani Sadiq - Gwarzon shekara

Hafsat Idris - Gwarzuwar shekara

Abubakar Bashir Maishadda - gwarzon mai shirya fim

Bello Hafizu - Gwarzon Mai bada umarni

Hannatu Bashir - Mataimakiyar jaruma a cikin shiri

Asabe Madaki - Ta samu kyautar Sabuwar jaruma wacce tayi fice

Ahmed Illiyasu Abdulmumin Tan-tiri - Matashin jarumi na shekara

Ibrahim Sule Katsina da Engr Babagana Abba Dalori sun samu kyauta ta musamman bisa gudunmawar da suke badawa a harkar fina-finan hausa.

Shirin 'Sarauniya'wanda Hassan Giggs ya bada umarni ya lashe kyautar .

A bikin gasar na bara fim na farkon da Rahama Sadau ta dauki nauyin shiryawa ta lashe kyautar shiri mafi burgewa.

Post a Comment

 
Top