Dan wasan Super eagles zaiyi ma kungiyar mahaifar sa goma ta arziki idan suka zura kwallo a ragar Kano pillars
Yace a ko wani kwallo da tawagar ta zura a ragar abokan adawar su kuma suka yi nasara a wasan kungiyar zata samu naira dubu dari daya.
Mai tsaron bayan ragar tawagar super eagles ta Nijeriya Shehu Abdullahi yace a shirye yake domin yi ma kungiyar mahaifar sa wato Sokoto united goma ta arziki na ko wani kwallo da suka zura a ragar Kano Pillars wasan tare na gasar Aiteo Cup.
A sakon faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Tuwita dan wasan yana mara ma kungiyar Sokoto United baya kuma yana karfafa gwiwar su wajen samun galaba.
Yace a ko wani kwallo da tawagar ta zura a ragar abokan adawar su kuma suka yi nasara a wasan kungiyar zata samu naira dubu dari daya.VIDEO: Dear Sokoto United.— Shehu Abdullahi (@OfficialShehu) September 13, 2018
Ahead of your @aiteogrp game against @pillarsfc this Sunday, I'm supporting the team with N100k per goal.
Emotional feelings for me, I started my career with home club, Sokoto United before joining @pillarsfc. Both teams face off this weekend@thenff pic.twitter.com/8EIacnI8q1
Dan wasan ya fara wasa a kungiyar Sokoto United da Kano Pillars gabanin zuwan sa kungiyar kasar waje.
Tsohon kungiyoyin sa zasu fafata a rukuni na biyu na gasar kofin Nijeriya ranar lahadi 16 ga watan Satumba.
Ga yadda sauran wasannin rukuni na biyu na gasar zata kaya;
Mighty jets vs Kwara utd
Osun utd vs Katsina utd
Ifeanyi ubah vs J. Atete
Elkanemi Warr vs Katsina utd feeders
Wikki Tourists vs Bayelsa utd
Cofine FC vs Sunshine stars
Crown FC vs Abia Warriors
Kogi utd vs Niger Tornadoes
Nasarawa utd vs Standard FC
Remo stars jnr vs Rivers utd
Yobe stars Plateau utd
Go round vs supreme court
Kebbi Utd vs Enugu Rangers
Post a Comment