Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta

Jarumar tana daya daga cikin manayna jarumai mata da tauraron su ke haskawa a farfajiyar Kannywood.
An haife ta ranar 21 na watan Febreru na shekarar 1993.

Kwarerwar da kuma himma da take badawa a wajen aikin yasa tayi fice cikin yan matan Kannywood.
Wasu daga cikin tsoffin fina-finanta akwai Sarki, 'Yar Tasha, Ana Wata ga Wata, Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da, Gwaska returns sauransu.
Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.
Kyakkyawar jaruma har yanzu bata yi aure ba amma akwai jita-jita da yadu shekarun baya cewa wasu daga cikin masana'antar Kannywood na neman ta da aure.
Daya daga cikin Nuhu Abdullahi ya bayyana cewa hakika yana son ta kuma zai so ta zama matar sa sai dai bai shirya yin aure ba.
Yace jarumar tana nuna masa biyayya kuma ta taimaka mashi sosai don haka yake matukar girmama ta.

Kuci gaba da karantawa:
👇👇