Daga Datti Assalafiy

Da farko ni Datti Assalafiy banji dadin kisan gilla da akayiwa wannan tsohon shugaban sojojin Nigeria Cheif Air Marshal Alex Badeh (rtd) ba, saboda mu bama goyon bayan kisan gilla ko da akan dabba ne balle mutum.

Kafin ya hadu da ajalinsa a yammacin jiya talata 18-12-2018 a hannun ‘yan bindiga, Alex Badeh yana fuskantar tuhuma a hukumar EFCC bisa zargin karkatar da makudan kudaden da aka ware don sayen makaman da za’a yaki ayyukan ‘yan ta’adda da kyautata walwalar rundinar sojin Nigeria zuwa aljihunshi da yayi a zamanin gwamnatin Jonathan.

Asirinsa ya tonu ne a ranar da shugaba Buhari ya saukesu daga mukaminsa ya kawo sabbi,
Hukumar EFCC ta kaddamar da mamaye a wani katafaren gida da Alex Badeh ya mallaka a birnin Abuja inda aka samu miliyoyin daloli da ya boye.
Hukumar EFCC ta zargi Alex Badeh da mallakar wadannan kadarori a dalilin sata , kadarorin da ya mallaka sune kamar haka.

1-Ya mallaki wani gida wanda kudinsa ya kai sama da naira biliyon daya a Wuse Abuja.

2-Ya sayi wani fili kudinsa ya kai naira miliyon dari shida da hamsin (N650m) a Wuse II Abuja.

3-Ya Mallaki wani katafaren shago a Wuse II wanda adadin kudinsa ya kai kusan Naira biliyon daya.

4-Ya sayawa yaronshi gida na tsabar kudi kimanin Naira miliyon dari biyu da sittin (N260m) a Kumasi Crescent Wuse II Abuja.

5-Ya bada kudi naira miliyon dari uku da talatin (N330m) ma wani mutumi dillalin gidaje mai suna Hon. Bature domin ya saya masa gida a Wuse II Abuja.

6-Ya bada kudi naira Miliyon dari biyu da sittin (N260m) ma wani dillalin gidaje mai suna Rabiu Isyaku Rabiu domin ya saya masa karamin gida a Wuse II Abuja.

7-Wani Mataimakin darakta a hukumar EFCC mai suna Aliyu Yusuf yace Alex Badeh ya cire zunzurutun kudi naira biliyon uku da miliyan dari tara (N3.9bn) daga asusun rundinar sojin saman Nigeria.

8-Daya daga cikin masu bincike na hukumar EFCC mai suna Abubakar Madaki yana bada shaida a gaban alkali lokacin da EFCC ta gurfanar da Alex Badeh a kotu yace; sun samu kudi a wani account na Alex Badeh wanda ya kai dalar amurka miliyon dari tara ($900,000) , sannan ya kara da cewa kudin da hukumar EFCC ta samu a asusun ajiyar kudi mallakin Alex Bade tun daga shakarar 2012 zuwa 2013 kudade ne da ya sace daga asusun rundinar sojin saman Nigeria lokacin da yake shugabancin rundinar.

9-Hukumar EFCC ta tabbatar wa kotu cewa bincikenta ya gano a duk karshen wata lokacin da Alex Badeh yake rike da mukamin shugaban sojojin saman Nigeria, yana fitar da kudi naira miliyon dari biyar da hamsin da takwas da dubu biyu (N558.2million) daga asusun rundinar sojin saman Nigeria zuwa cikin wani asusun ajiyar kudi mallakinshi.

Wannan kadan ne daga cikin abinda Alex Badeh ya aikata lokacin da yake rike da mukamin shugaban sojojin saman Nigeria, daga bisani Jonathan ya daukeshi daga wancan matsayin ya kara masa matsayi zuwa shugaban sojojin Nigeria gaba daya (Cheif of Defence Staff), Allah ne kadai ya san satar da yayi a wannan matsayin.

Jama’a a karkashin shugabancin su Alex Badeh ne kungiyar Boko Haram ta karbi dukkan garuruwan da ta karba a tsakanin jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Tunda ake a tarihin Nigeria ba’a taba yin wani lokacin da dakarun sojin Nigeria suke kukan babu makaman yaki suna guduwa daga fagen daga ba kamar a lokacin su Alex Badeh.
Tunda ake a tarihin Nigeria ba’a taba yin wani lokaci da aka fitar da makudan kudin da za’a sayi manyan makaman yaki na zamani amma sai aka karkasa kudin aka cinye kamar a lokacin su Alex Badeh ba.

Tunda ake a tarihin Nigeria ba’a taba yin wani lokaci da shugaban sojojin Nigeria ya sace biliyoyin daloli wanda za’a sayi makamai ya kai gidanshi ya tona rami ya bunne kudaden ba kamar a lokacin su Alex Badeh.

A dalilin kudin da su Alex Badeh suka sace ya taimakawa ‘yan ta’addan Boko Haram sukayi ta’addancinsu yadda sukaga dama, har Shekau yana cika bakin cewa shi duniya yazo yaka ba Nigeria kadai ba, dubban rayukan ‘yan arewa ya salwanta a dalilin satar kudin makamai da akayi.

Ya kai ‘dan arewa menene abinda zai dameka don wani mutumi ya girbi sakamakon abinda sune sukayi sanadiyyar wanzuwarsa a cikin ‘kasarmu Nigeria?
Don Nigeria ta rasa irin wadannan mutane da sukaci amanar tsaro, sukaci amanar Nigeria da ‘yan Nigeria, wallahi bai kamata wani ‘dan arewa ya daga hankalinshi ba, tsakaninmu da su sai dai Allah Ya isa.

Allah Ka isar mana Amin.

Post a Comment

 
Top