An zabi dan wasan kwallon kafa na Egypt kuma na kungiyar Liverpool Mohamed Salah a matsayin dan wasan da ya fi kowanne taka leda sau biyu a jere.
Dan wasan mai shekara 26 ya doke Medhi Benatia da Kalidou Koulibaly da Sadio Mane da Thomas Partey, ya lashe lambar.
“Abun farin ciki ne,” Salah ya shaida wa BBC.
“Zan so a shekara mai zuwa ma in sake yin nasara. Ina farin ciki da yin wannan nasara.”
Dan wasan da ya lashe lambar yabo ta Gasar zakarun Turai na bana ya zira wa Liverpool kwallo 44 a raga a wasanni 52 a kakar da ta wuce kuma ya taimaka wa kungiyar kai wa zagayen karshe a kasar Zakarun Turai.
“Ko wane lokaci, ina ji kamar na ci kwallo, ina taimakon kungiyar kulob din ya samu maki a gasar, wannan a koyaushe abu ne mai faranta rai.”
Ya ci wa Masar kwallo sau biyu a gasar cin kofin kofin duniya ta bana.
BBC ta samu kuri’u sama da 650,000 a bana – wanda wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu.
Salah ya zama dan wasa na farko da ya lashe kyautar sau biyu tun bayan JayJ Okocha.
Tsohon dan wansan na Chelsea ya sanya hannu da kulob din Liverpool bayan ya baro Roma a kakar 2017. Ya ci kwallo 15 sannan ya taimakawa Roma ta ci kwallo 11, wacce ta gama gasar Seria A a mataki na biyu.
Ya fara wasansa a Liverpool da kafar dama, inda ya zura kwallo 19 a raga a wasanni 24.
Ya share nasarorin da aka yi a baya na kwallaye 31 a wasa 38 a kakar gasar firimiya, wadanda Luis Suarez suka ci a 2013-14, da Cristiano Ronaldo a 2007-08, da kuma Alan Shera a 1995-96.
Mohamed Barakat (2005) da Mohamed Aboutrika (2008) su ne sauran ‘yan Masar din da suka lashe gasar.


Source from: HAUSALOADED.COM

Post a Comment

 
Top