daga farko har karshe a ji hujjojinta. Muna so ki fara da bayyana mana sunanki da cikaken tarihin rayuwarki a takaice? Sunana Janet Thomas Rogers. Daga Southern Kaduna. Ni ‘yar Bajju ce. Na yi makaranta a Jami’ar Lagas. Daga nan na taho Kaduna domin na fara sana’ar fim. Na taso a Ugwar Rimi Lowcost, kuma na yi karatun Firamare ta Unguwar Rimi, daga nan kuma na yi makarantu Sikandire har guda uku. Makarantar Sikandiren Gwamnati dake Marmara, da makarantar Sikandiren Gwamnati ta Wukari, sai kuma ‘Our lady of Fatima Secondary school sabo Kaduna. Amma na gama a GGSS Kankiya ta Jihar Katsina. Mu biyar ne a wurin iyayemmu, ni ce ta hudu. Iyayena Allah ya yi masu rasuwa, hakan ya sa ni na biya da kudin makarantata, ina aiki ina makaranta a Legas. Me ya ba ki sha’awar shiga harkan fim kuma da Wanne kika fara? Ai dama lokacin da ina Firamare akwai wanda ya zo daga Cocimmu wai mu zo mu dinga wasan kwaikwayo, wato rawa da Dirama a wurin Mallama Ruth Sanke a Space 2000.

A lokacin Space 2000 yana kusa da ‘Capital School Malali Kaduna.’ Wani sa in za mu taka da kafa daga Ungwar Rimi zuwa Malali domin ‘Rehearsal’. A nan naso harkan Fim, domin a lokacin ina tare de abokai na da mata da maza, wayyo wasun su yanzun Allah ya yi masu yasuwa, akwai Paul wanda shi ya kai mu Space 2000. A lokacin za mu kan zuwa makarantu daban-daban mu yi wasa. To bayan haka sai na fara makarantar Sikandire ta kwana, da na dawo a lokacin an mayar da Space 2000 Barnawa. Sai na ce bari na gama makaranta ta duka daga baya sai na dawo fim. Amma ‘Accounting’ ne na karanta a makaranta. To bayan da na gama sai na dawo Kaduna in da na fi ganewa, a nan na hadu da Oga Gabby Gabriel Okotie, a lokacin shi ne ‘AGN Chairman Kaduna chapter,’ lokacin yana daukar shirin fim din ‘Magarwata’ sai na fara da su. Janet ga ki ba Bahaushiya ba, kuma ba Musulma ba, me ya ba ki sha’awar shiga fim din hausa Ni a ganina duk mutumin da ya fito daga Arewa to ko Kirista ne ko Musulmi duk Bahaushe ne daya ne, ko a zuri’ar mu muna da Muslimai da Kiristocin. Haka kuma da yawammu Kiristocin Arewa Hausa muke yi da junanmu. Wallahi ai ba ki sani ba, hatta yare na, ban iya ba, amma gashi na yi makaranta a Kankiya Jihar Katsina. ni ai na fi tarayya da Musulmai ne, ga bokaina su Aisha Ruma, Umma Fadilah, Bilkisu Tuge, Aisha Shehu Musa Yar’adua da sauransu. Sannan babban mataimaki na shi ne Aliyu Rabiu Kurfi tsohon Kwamishinan ilimi na Jihar Katsina, kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kurfi. Shi ya sa na yi makaranta a Katsina. Kuma kin ga a kudu sun dauka duk mutumin da ya zo daga Arewa ai Bahausa ne, gashi Ogana Gabby da na yi aiki da shi Hausa fim yake yi. Ko za ki Lissafo mana fina-finan da kika yi a Kannywood da Nollywood? To manyan ayyuka da na yi su ne Magarwata, Tsirin, Tsaka, Burin duniya, da ake nuna wa a Africa Magic Hausa da Dadin Kowa a Startimes da sauransu. Sannan na yi ‘Mechanic Workshop. Arc of my Destiny.’ Wedding Nights, Boon of being righteous, Shattered foundation, Lost happiness. Battle ground, da ake nuna shi yanzu a African Magic Showcase, da sauransu. Menene banbanci tsakanin kannywood da Nollywood? Banbancin Kannywood da Nollywood yana da yawa, amma bari in fadi na Kannywood, kungiyar Jaruman Hausa, sanna nollywood na turanci. Kuma a Kannywood sai da ka iya Hausan Kano, amma ki ga nollywood ba su banbanta yare, za ki ga Yarbawa da Iyamurai har dai Hausawa cikinsu, in dai har ka iya aiki, za a yi da kai.

Kin ga ni ‘yar Kaduna ce, kuma a Kaduna muna da Musulmai da Kiristoci, haka kuma a kano Adamawa, Jos, da sauran wurare a Arewa. Don haka bai cacanta ana nuna banbancin addini ba. Sanna kuma masu shirya fim ‘Producers’ na nollywood da kyar su zo yin aiki a Arewa, domin suna ganin Arewa na kannywood ne, kin ga mu Kiristoci ba ma nan ba mu can. Matsala ta shi ne wasu jaridu da Talabijin kamar BBC Hausa, suna daukan labaran jarumai masamman Musulmai shi ya sa da yawan Kiristoci suna canja sunayensu zuwa sunayen Hausa domin su samu shiga. Kin ga har Segun Arinze ya taba gaya mun wai har in ina so a sanni a Arewa sai dai na canja sunana, da yake a Arewa ya girma kinga bai dace ba. Shi ya sa ina godiya da LEADERSHIP Newspaper da damar da suka ba ni, gaskiya ina matukar godiya Allah ya albarka ci jaridarku. Ga shi kuma da yawa labaran Hausa fim, labarin tahirin Hausa kawai ne da yawansu, ki ga wasu a kasar waje ba su san akwai Kiristoci a Arewa ba. Sun dauka dukkan ‘yan Arewa Musulmai ne. Amma in dai har za fara labarai wasu wurare a Kasar Arewa, kamar tarihin gwarawa, Tarihin ‘Nok Kingdom,’ da sauransu. Wallahi da yawan mutane Kasar waje daga wasu yararruka za su fara so kallon Hausa fim. Kinga na hadu da ‘Ambassador of culture and tourism of Hungary’ na Nijeria.

Omotunde Komolafe, kuma shi ke da ‘Iroko Awards London, da Adire Festibal, da yake matarsa Baturiya ce, ya yi mamaki da wai har a kwai Kiristoci a Arewa, cewa suna ganin duk ba mu waye ba. Na gaya ma sa cewa ai ko cikin Musulmai muna da wanda suka waye da yawa, don dai labaran da a ke nuna wa ne. Ya ce zai iya taimakon wasu daga cikin masu shirya fim din Hausa su yi premier fim na su a kasar turai don a sansu. Wace irin wayewa suke ganin Musulmin Arewa ba su yi ba? Kin ga banbanci Musulmin Arewa da na Kudu shi ne rufe sirrin jiki, wato ki ga Musulmai Arewa a dole sai sun yi lillibi, amma Musulman Kudu ba lallai ba ne a a gare su, kuma kin ga lullubi su da ban yake da na Arewa, don haka sun dauka ce wa wanda ba su shiga makaranta ba ne su ke irin shiga nan. Kuma ki ga in kin je garin Legas, za ki ga dayawa ‘yan Arewa sai da aikin diban ruwa, ko aikin gabi. Ko shoe shiner, wato gyaran takalma, a hakan ne su ke gani yawanci su ba su waye ba, shi ya sa kuma suke nuna rai nin wayo.

Ai ma’anar aboki ko mallam da suke kiran Hausawa kenan. Idan za a yi fim na al’adun wasu yarukan Arewa da ba Hausawa ba, da yarukan za a yi ko da Hausa? Ai ya danganta da yanayin fim din, domin kamar fim na Dan Yarbawa, ana yi ne a hausa amma da muryar Yarbanci, kuma haka Dan Iyamiri da Hausa a fim din, sako da fim din ke nuna sh a nan shi ner Arewa fa akwai Yarbawa da Iyamarai, kuma amma zaman ana tarayya da juna. Kin ga kamar fim na turanci, so dayawa za ki ga maigadi yana turanci ama da muryan hausa…wato caraktarization kenan, domin annan mai kallo za gane ce wa fa, a nan garin, akwai wasu yare da suke wurin. Haka kuma in zan yi fim na zallan yare, na san zallan yare ne, amma kuma a zamin nan, ba kowa ke jin yare sa. Shiyasa in kina kallon fim na iyamarai a african magic, wani sa’in sai su hada yare da turanci. Gashi na baki misalin fim na ‘Kauna’, fim na yaren bajju ne amma gashi nan an yi ta a hausance.
 kuma casts din musulmai da christoci har da wasu yare da ba arewa ba. Har ila yau munaso ki fada mana wani masanaantar ce kikafi jin dadin aiki dasu tsakanin kannywood da Nollywood? Amma ki yin tambaya ma nauyi, za ni ce dukan su ina jin daddin aiki da su. Wallahi in dai har za a dai na nuna banbanchi wallahi dukan mu za mu ji daddin tarayya da junarmu…kuma in dai Kannywood za su dai na sa lailai sai hausan kano, domin a arewa kowa yana da yanda su ke furta hausansu. Ba ki ganin Hausar Kano ita ce aka fi fifitawa a daidaitacciyar Hausa (standard Hausa) shi ya sa furodusoshi da daraktoci suka fi nacewa a kanta? Misali kin ga, akwai wani producer a kaduna christin ne, mai suna Kantiok Joel fim nasa labarin tahirin bajju ne, ama ya yi amfani da christoci tare da musulmai kamar Ibrahim daddy. Haka kuma wata mallama Zeena Bako ta fitar da fim mai suna Kauna wanda ke maganar aladan southern kaduna, ama tayi aiki da hausawa da kuma yan yare… Sannan kuma ki ga fim kamar hakunde da aka hada yan hausawa da yan fim na turanci, mai zai sa kuma a na ce sai hausan kano. Gashi in kin duba fim na yarbawa a misali, yaki ga wasu sun fito gada ondo. Wasu da ogun. Ibadan kuma yarbawan su ba daya bane ama ba a na ce dole, sai yarbawa wuri ka za….kinga hadai hadai yare a fim wani sa’in ke sa fim yayi dadi kuma ya ke sa hadin kai da zama tare. Wani kalubale kika taba fuskanta a tsakanin wadanan masana’antar tare kannywood da Nollywood? To a nollywood ne dai a kwai mani zan ce shi fake producer a garin kaduna suna sa Michael Yusuf Michael, ya so ya wulakanta da ni domin yana son in ba sa kudi ya hada yayi fim kuma yana so yayi lallachi da ni…amma kuma ban basa da ma ba. Kuma da ya ji ina aiki da Oga Gabby, sai ya bar ni. Amma kuma a kannywood ina da abokai da suna ban labarin edperience ta su… banbanchi shi ce, kin ga nollywood annan lagos, suna da directors da producers dayawa don haka in wani ya hana ki da aiki domin bai samu daman lallaci da ke ba, za ka iya samu aiki a african magic kamar tinsel ko battle ground wanda ba wani de zai sa ki dole ki kwana da shi don ya baki aiki. Eberything is based on credit. Ba za ki ji director ko producer ko pm a mnet yana gaya maki ki sa me ni a hotel zaka ba…ama kin ga kannywood n nollywood a arewa… producers ba su da yawa, kuma don haka sun san junar su, dun haka za su iya hana ki or ko ka aiki in ba su son ki. Ko kuma in ki yi masu laifi. Tsakanin fim din Hausa da na turanci wanne ne ya fi ba ki saukin dauka? Ni dukan su suna da wuyarsu da saukinsu ya dangata da yadda labarin yake. Ko Kina da sha’awar ki zama mai ba da umarni, ko mai shiryawa a fim dinki, Kuma na turanci kike sha’awar yi ko na Hausa? In sha Allahu ina shirin yin fim a shekara mai zuwa tare da aboki na domin yana da ‘Camera Drone’ guda biyu sai ya ce mu yi aiki tare sai mu raba ribar, don yana aiki a wani babban offishi don haka ba ya so sunansa ya nuna a aiki. Muna jiran labarin ne daga wurin wata babban marubuciya a Kaduna wato Magdalene Musa. Kuma fim daya za mu yi na tuaranci da Hausarsa gaba daya kamar ‘The Johnson’s. Janet wace shawara Za ki ba wa mata masu shawar shiga harkan fim? Shawarata ita ce su lura da kyau da ya ke wasu masu shirya fim din za su yi masu zakin baki ce wa za su zamar da su Ali Nuhu ko Rahama Sadau a rana daya, wannan ma ai abin dariya ne, kar su kuskura su amince da su, sannan su yi hakuri kuma su dogara ga Allah za su yi suna. Sai kuma kafin su shiga, su yi rajista a kungiyar, sannan su samu wanda ya dade kuma wanda ya ke da zuciya mai kyau ya zama mai ba su shawara. Da ya ke ni ina da mutane da yawa, wasu a facebook su kan tunkare ni da ce wa suna neman shawara, domin suna son yin aikin fim, misali wata Princess Ladee Bako, a facebook ta sa me ni cewa tana son ta yi aikin wasa, haka na ba ta shawara ta yi rajista da Agn Kaduna, ga ta yansu za ta yin aikin fim na Agn. Wallahi yanzu kafin ta je wani ‘Audition’ sai ta tinkare ni. Haka kuma sauran kuma in sun yi ladabi da biyayya su yi ni sa. Mun gode sosai da hadin kan da kika ba mu Nima da gode da damar da kuka ba ni

©leadershipayau.com

Source from: HAUSALOADED.COM

Post a Comment

 
Top