Daga Bello Muhammad Sharada

Ni na gaji da bada labarin kisan kiyashi da ake yi wa jama’ar Zamfara da sace mutanen da yin garkuwa da su da fyade da ake yi wa ‘yan mata da matan aure da kwace dukiyar al’ummar jihar da karfin zalunci da ta’addanci.

Labaran sun isa haka. Jinsu ya ginshe ni saboda takaici.

Aikin farko na kowacce gwamnati ko tarayya ko jiha ko karamar hukuma shi ne kiyaye ran jama’a da dukiyar da suka mallaka.

Akan Zamfara duk hukumomin sn kasa.

Ga hanyoyin da za a bi a samu sauki a Zamfara:

1. Gwamnati tarayya ta sauke ministan tsaro Mansir Dan Ali dan asalin jihar Zamfara, daga kan mukaminsa. A nada wani sabo.

2. Na biyu gwamnatin tarayya ta sauke tsohon soja Janar Abdurhaman Dambazau, dan asalin jihar Kano kuma ministan harkokin cikin gida daga kan mukaminsa. A nada wani sabo.

3. Na uku gwamnatin tarayya ta sauke Janar Yusuf Buratai dan asalin jihar Borno kuma shugaban rundunar sojojin kasa daga mukaminsa. A nada wani sabo.

4. Na hudu gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a jihar Zamfara kuma ta sauke gwamna AbdulAziz Yari daga kan mukaminsa ta dauko wani tsohon soja dan asalin Zamfara ta bashi riko na jihar na wata shida.

5. Na biyar a kawo sabon shugaban tsaro daga soja da zai jagoranci yaki da wadannan miyagun. Jama’ar da zasu yi wannan aiki su hada da kato da gora, da gogaggun ‘yan sanda da jami’n asiri, amma a basu makamai na zamani da kayan binciken tsaro da duniya ke amfani da su, a rika sallamar sojoji da sauran jami’ai albashi ba makara kuma duk wani tsarin jin dadinsu kada a rika jinkiri, inzai yiwu a ninka shi,kuma a ware wasu kudade masu kauri duk wani wanda wannan rikici ya rutsa da ransa za a biya ahalinsa. Misali duk soja ko jami’in tsaro ko dan sintiri da ya rasa ransa a wannan sabga za a baiwa iyalinsa miliyan 50, duk kuma wanda ya yi bajinta zai samu gwaggwaban lada, sannan za a karrama shi.

6. Na shida, a yi maza-maza a samar da babban asusu da zai yi aiki da hukumar NEMA domin jin kan jama’ar da suke cikin fargaba da gudun hijira da wadanda suka tafka asarori masu yawa sakamakon aikin wannan miyagun.

7. Na bakwai a kafa kwamitin masu ruwa da tsaki na Zamfara da zasu rika bada shawara kan wannan mas’ala da dabarun kawo karshenta

8. Na takwas shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na kwamanda in cif ya kai ziyarar yini biyu a jihar Zamfara, amma lallai ya ziyarci wani banagare na dajin Dan Sadau da garin Dan Kurmi da Dan Gulbi da Dan Jibga. Zai yi kyau ya je Kauran Namoda da wani yankin Tsafe da Anka da Shinkafi da Mafara, ya ji kuma ya gani daga ainihin mutanen, kada ya tsaya a Gusau barikin soja.

9. Na tara ‘yan siyasa su guji sanya siyasa cikin mas’alar Zamfara, a madadin haka su hada karfi waje guda a tunkari kawo karshenta.

Post a Comment

 
Top