Wasu ‘yan majalisar wakilai sun baiwa hammata iska, yayin da wasu ke wakar habaice-habaice a zauren majalisar suna cewa “ba a samun ‘yanci sai da gwagwamarya, sai da gwagwarmaya, lokacin ‘yanci ya yi”.
Wadanda suka baiwa hammata iskan su ne, Bashir Babale da Duoye Diri. Majalisar ta hargitse ce sa lokacin da wasu ‘yan majalisar suka fitar da kwalaye (masu dauke da rubuce-rubuce), sannan wasu a cikinsu suna yagawa. Sai dai komai ya natsa daga bisani.
Post a Comment