Daga Bello Muhammad Sharada

A cikin littafin da ya rubuta ‘Not My Will’, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi suka ga Alhaji Shehu Shagari cewa bai shirya ya mulki Najeriya ba, jajibo shi kawai su Makaman Nupe da Abdurahman Okene suka yi. Obasanjo yana ganin Shagari ba shi da kwarewa da gogewa da zai mulki kasar nan, Najeriya a ganin Obasanjo tafi karfinsa.

Amma shi kuma Alhaji Shehu Shagari ya rubuta a nasa littafin ‘Beckoned To Serve’, cewa rainin wayo ne da fadin rai na Obasanjo wanda babu abin da ya iya kuma babu abin da ya sani sai faretin soja da harba bindiga, ya shiga soja a kurtu, kuma bai san siyasa ba, bai san mulki ba, kuma bai iya hulda ba.

A binciken da nayi, a wannan takaddama, Shehu Shagari ya fi Obasanjo gaskiya. Dalili shi ne, an rantsar da Shagari a matsayin shugaban kasa na farko a tsarin shugaban kasa mai cikakken iko ranar 1 ga watan Oktoba 1979, a lokacin shekarar 53.

Kafin zamansa shugaban kasa, Shagari a gidan sarauta ya taso, sannan ya zauna da Turawan mulkin mallaka, ya yi aiki da su a matsayin malamin makaranta. Ya shiga rigimar kwatowa Najeriya ‘yanci dan kishin kasa ne. Da shi aka kafa NPC, kuma da shi aka kafa NPM ta rikide zuwa NPN. Ya yi takarar kansila da majalisar wakilai. Da shi Turawa suka fara tsara tsarin mulkin Najeriya na Richard da Macpherson.

A tsakanin shekarar 1958 zuwa 1978 Shehu Shagari bayan sakatare na Tafawa Balewa da ya yi a lokacin Balewan yana firaminsta, ya rike mukamin minista a ma’aikata goma. Har shugaban bankin duniya Shagari ya rike. Duk wani aiki da aka yi da wanda aka tsara domin gina kasar nan da hannun Shehu Shagari a ciki, Janar Murtala Ramat Muhammad ya gayyaci Shagari cikin gwamnatinsa ya ce ya gaji, a baiwa wani, kaga kuwa daidai ya fada da ya ce Obasanjo rainin wayo ne da shi.

Allahu Akbar, Shehu Shagari ya koma ga Allah a jiya bayan gajeruwar rashin lafiya. Yana da shekara 93, ya bar duniya.

A tsohuwar Najeriya mai jiha 19 babu birnin da zaka je baka samu unguwa ba da sunansa. An yi gidaje ne gwamnatinsa a unguwar. A wasu guraren an sanya wa garuruwa sunansa, an yi manyan gonaki ne a garuruwan a gwamnatinsa.

Ina karami a ajin firamare mahaifinq ya taba sayo min littafin ‘Wkar Najeriya’ mai baiti dubu, wacce Shagari ya wallafa kuma ake amfani da ita a kasar Hausa kuma na ga Shehu Shagari a Filin Mushe taron kamfen na siyasa, a wajen taron NPN a lokacin na iya rike wa Dan Masanin Kano ya yi magana. A wannan gurin na taba halartar kallon taron PRP wanda Aminu Kano ya yi jawabi. Naga Alhaji Muhammadu dan Kauye a gurin. Nan ce mahaifata.

Amma a shekarar 2001 na taba zuwa na ziyarci Shehu Shagari a gidansa ina matsayin editan jaridar AT-TAJDID. A kofar gida na tambaya ko yana nan, aka gaya min baya nan, na bar katina da kwafin jarida, dana dawo da magarib, ya umarci na shigo. Bamu yi intabiyu da shi ba, amma mun yi hira ta kasa da shi tsawon awa guda, ya rako ni muka yi sallama. Na taba neman ganin Bashir Tofa a gidansa na Gandu a Kano sau uku ina zuwa a shekarar 1994-95, amma ya gagara. Wannan yana nuna maka saukin mu’amalar Shagari. Mutumin da ya rike duk wadancan mukaman amma ya koma ya rike kansila. Da kyar aka shawo kansa ya yi takara a 1979, kuma a lokacin naira 200 ce kawai abin da ya kashe a harkar takararsa gaba daya. Takarar shugabanci kayan al’umma ne.

Bana jin akwai wani shugaba da Najeriya ta yi da ya kai Shagari amana da gaskiya da aiki cikin sanin makama, kuma wanda ba a taba zarginsa ba da cin hanci. Bana jin akwai shugaba mai saukin kai da bin ka’idar aiki kamar Shagari. Ya bar duniya gidansa bai kai na Babangida ba, gonarsa ba ta kai ta Obasanjo ba, hannun jarinsa bai kai na Buhari ba, asusun ajiyarsa bai kai na Abdusalami Abubakar ba, balle na marigayi Sani Abacha. Amma kuma dan siyasa ne da ya rike mukamai da duk ya fi nasu.

Gaskiya Alhaji Shehu Shagari ya bada gudunmawa matuka a wajen gina kasar nan. Da ba a yi masa juyin mulki ba shekarar 1983 da yanzu muna kafada da kafada da Singapore da India da Brazil kai har da Germany.

Najeriya tayi babban rashi. Jikansa Bello sun taba kafa kungiya da sunan arewa, suka sanya shi a uban kungiya, ya ce su cire sunansa, duk abin da ba na Najeriya bane gaba daya baya ciki. Najeriya ta shiga halin da take ciki a yau saboda rashin masu hali irin na Shehu Aliyu Usman Shagari ne.

Post a Comment

 
Top