A yau ne Gwamnan Jahar Bauchi Mohammed A. Abubakar ya je masallacin babban Malamin Addinin nan wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin gabatar da Sallar Juma'a. Isar shi keda wuya, da mutane suka gane shine sai waje ya dauka, mutane manya da yara suka yi dafifi domin ganin shugaban su, wato Gwamna M.A Abubakar da kuma gaisawa dashi. Haka yayi ta gaisawa da mutane, shi farin ciki, suma farin ciki.

Shigar sa masallacin keda wuya, ya gabatar da Sallar nafila sannan ya zauna domin sauraron huduba. Bayan idar da Sallah, Mai Girma Gwamna ya tashi ya gaishe da Shehi cikin ladabi da biyayya (kamar yadda ya saba).

Sheikh Dahiru Usman ya daga hannu sama ya gabatar da adduoi ga kasa, Jahar Bauchi da kuma Mai Girma Gwamna. Yayi adduan tsari, nasara da dukkan alheri wa Mai Girma Gwamna. Daga bisani yayi godiya ga Gwamnan bisa yadda yake mutunta kowa, ya rike kowa a matsayin nasa.

Kamar yadda aka yi lokacin zuwansa, haka aka yi lokacin fitan sa. Jama'a da dama suka ta gaisawa da Gwamnan da yi masa fatan alheri.

Allah Ya tabbatar mana da alheri.

Hotuna daga Galajen Gwamna

Daga Shamsuddeen Lukman Abubakar
Mataimaki na musamman ga Mai Girma Gwamna a fannin Sadarwa






Source from: HAUSALOADED.COM

Post a Comment

 
Top