Daga Yaseer Kallah

A jiya ne Allah ya amshi rayuwar dattijon kirki kuma tsohon malamin makarantar nan mai suna Alhaji Sanda Kaita na jihar Katsina.

Jaridar Katsina Post ta fitar da rahoton cewa an binne dattijon a makabartar Rimin Badawa bayan an masa sallah a gidansa da ke Filin Samji, bayan ‘Multipurpose Hall’, Kofar Durbin babban birnin Katsina.

Malam Jaafar Sabuwar Kasuwa ne yai masa Sallah, inda tarin al’umma ciki har da kwamishinan kasuwanci, Abubakar Yusuf da tsohon sanata Abba Ali suka halarta.

Malam Jaafar ya masa addu’ar Allah ya gafarta masa tare da sanya wa iyalinsa juriya da hakurin rashinsa.

Marigaya Kaita, dattijan kwarai kuma tsohon malamin makaranta, wanda ya rasu yana da shekaru 88, ya taba zamowa shugaban makarantar sakandaren gwamnati ta Katsina ‘Government College’, GCK.

Wasu dalibansa a makarantar sun hada da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa, Sanata Abba Ali, Inusa Saulawa da Tanimu Gidado.

Post a Comment

 
Top