Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya bayyana cewa alakarsa da dan wasan Real Madrid ba wata alaka bace mai karfi domin ba abokai bane kuma basa haduwa sai a wajen bada kyaututtuka.
Yaci gaba da cewa bashi da wata babbar alaka da Ronaldo kuma su ba abokai bane domin abokai sune wadanda suke yawan haduwa kuma suke tattauna abu-buwan da suka shafesu amma basa yin haka da Ronaldo domin a shekara sau daya suke haduwa suyi Magana shine a wajen bada kyauta domin idan an hadu a filin wasa kowa kungiyarsa yake karewa.
Ya ci gaba da cewa kuma kungiyoyin Manchester City da Paris Saint German a yanzu sune barazana a kwallon kafa a duniya domin karfinsu yakawo kuma babu kungiyar da bazasu iya dokewa ba. Ya kara da cewa a halin yanzu akwai manyan yan wasa matasa masu tasowa irinsu Neymar da Mbappe da Suares wadanda nan gaba suma zasu iya lashe irin kyaututtukan da suka lashe tsakaninsa da Ronaldo.
A karshe yace har yanzu bai yarda cewa sun yiwa Real Madrid fintikau ba a gasar laliga domin sunada manyan ‘yan wasa kuma har yanzu ba’a gamaba komai yana iya faruwa a nan gaba.
Source from: HAUSALOADED.COM
Post a Comment