Daga Datti Assalafiy

Sanata Dino Malaye yayi zargin cewa Shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP Ibrahim K. Idris ya shirya masa makarkashiya zai kamashi ya masa allurar mutuwa, tuni wadanda zasuyi aikin sun fara shirin, kuma dalilin da yasa kenan shugaban ‘yan sandan na Nigeria ya canza kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi, don haka a jira aga abinda zai faru inji Dino Malaye kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter

Hakika Allah Ya jarrabi ‘yan Nigeria da miyagun sanatoci a matsayin wadanda suke wakiltar ‘yan Nigeria, imbanda kaddara da kasancewar Nigeria hadin gambiza ce me zai kawo su Dino Malaye fadar majalisar Dattijai?

Babu shakka Dino Malaye ya kwankwadi giya mai karfin gaske ta bugar dashi kafin ya wallafa wannan rubutu mai matukar hatsari wanda na tabbata sai Maigirma shugaban ‘yan sanda IGP Ibrahim K. Idris ya kalubalanceshi a inda ya dace.

Kuma jama’a a lura sosai, tunda ake a tarihin Nigeria ba’a taba yin shugaban ‘yan sanda da yaja daga da miyagun sanatoci ba kamar wannan? ya kama Dino Malaye, yayi yunkurin kama sanata Bukola Saraki, kuna tsammanin inda ace yana karban na goro a hannunsu zai iya jan daga dasu?

Ku fahimci dalilin da yasa hankalinsu yayi matukar tashi bayan shugaba Buhari ya kara masa wa’adin watanni 6 kafin yayi ritaya, wanda hakan yana nufin sai an kammala zabe, su Dino Malaye da jam’iyyar su ta PDP sai da sukayi alwashin zasu gurfanar da shugaba Buhari a kotu matukar bai sallami IGP Ibrahim K. Idris ba wanda zaiyi ritaya a watan da zamu shiga na January.

Yanzu kuma Dino Malaye ya fitar da wannan bayani na sharri saboda akwai abinda sukeso su cimma akan maigirma shugaban ‘yan sandan ‘kasarmu Nigeria.

Allah Ka tsare Nigeria da ‘yan Nigeria daga sharrin miyagun mutane.

Post a Comment

 
Top