‘Yar Shekara 9 ta yi karar shugaban makaranta bisa tirsasata cire hijabi

Wata daliba ‘yar shekara 9 a jihar Ogun ta shigar da gwamnatin jihar da shugaban makarantarsu kara kotu bisa tirsa cere hijabi da suka yi, wanda ta bukaci kotu da ta karba mata Nera Miliyan Daya a matsayin kudin fansa.

Yarinyar mai suna Aisha Abdul-Aleem, daliba ce a makarantar Gateway Junior Secondary School. Aisha ta shigar da shugaban makarantar, Principal Kushimo da gwamnatin jihar kara ne gaban babban kotun Isabo dake birnin Abekuta.

Majiyarmu ta Daily Post, ya ruwaito cewa, Mahaifin Aisha, Muhammad Abdul-Aleem ya bayyana cewa Aisha ta shigar da shugaban makarantar kara ne bisa tilastata da ya yi da ta cire hijabi tare da hanata shiga aji a wannan rana.

Lauyan Yarinyar, Olusoji Odutan ta bayyana cewa hakan da aka yi mata ba daidai ba ne sannan ya sabawa dokar kasa hana hana dalibi shiga aji domin wata doka da da gwamnati kafa na hana daliban gwamnati sanya hijabi a fadin makarantun jihar.

Lauyar ta kara da cewa, hana dalibar sanya hijabi ya sabawa ‘yancinta.

Post a Comment

 
Top