An Hallaka Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Air Marshal Alex Badeh
Daga Yaseer Kallah
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ba sun hallaka tsohon babban hafsan tsaron Nijeriya, Alex Badeh.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun masa kwantan bauna a kauyen Gitata, kan titin Keffi zuwa Badeh.
Rahotannin sun kuma ce rundunar soji ta samu gawarsa tun tuni.
Badeh tsohon sojan sama ne mai tauraruwa hudu wanda ya kasance shugaban sojin sama na 18 daga 4 ga watan Oktoba, 2012 zuwa 16 ga watan Junairu, 2014. Bayan nan shi ne ya zamo tsohon babban hafsan tsaro na 15 daga ranar 16 ga watan Junairu, 2014 zuwa ran 13 ga watan Yuli, 2015.
Post a Comment