Ibrahim Baba Suleiman

….Ta kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen Harkokin tsaro a kasa.

A yammacin yau Laraba shugaban kungiyar IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna alhini da jajantawa ga kungiyar IZALA Jos bisa hadarurruka da motocin wa’azi sukayi bayan tashi daga wa’azin kasa a garin dutse dake jihar Jigawa a karshen makon da ya gabata.

Sheikh Lau ya kara mika jaje ga shugaban majalisar Malamai ta IZALAR Jos Sheikh Sani Yahaya jingir bisa garkuwa da ‘Yan Agajin IZALA da wasu mutane sukayi a hanyar su ta komawa gida garin Issa
a jihar sokoto. Sheikh Lau yace wannan abun a tausaya ne kwarai da gaske.

Shugaban IZALAR ya umurci limamai na juma’a da na kamsu salawat a fadin Naijeriya da su fara yin Al-Qunut a lokutan salloli kamar yadda yazo a sunnah, domin neman gudunmawar Allah a wannan masifa.

A karshe shehin Malamin yaja hankalin gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukan mataki a wannan fanni na garkuwa da mutane kafin abun ya zama abun da ya zama, Duk kuwa da ana kokari wajen inganta tsaro.

Sheikh Bala ya mika sakon ta’aziyya da jaje ga wadanda suka samu hadari a hanyarsu ta komawa gida daga wajen wa’azi na jihar Katsina, da Jigawa, tare fatan Allah ya baiwa wadanda sukaji rauni sauki, ya jikan wadanda suka rasu.

Post a Comment

 
Top