Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya yi ikirarin cewa rashin tsaro ya karu matuka a lokacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Dogara ya yi kira ga al’ummar yankin arewa maso gabas su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.
Rahotanni sun ruwaito cewa, Dogara ya bayyana haka ne a jihar Gombe yayin da jam’iyyar PDP ta ke gudanar da gangaminta a yankin.
Dogara yace lallai Nijeriya ta shiga wani irin yanayi a karkashin gwamnatin Buhari, domin a cewar sa a yanzu kimanin yara miliyan 13 ne basa zuwa makaranta, kuma a cikin su yara miliyan 1 da dubu dari 3 sun fito ne daga jihar Bauchi.
Yakubu Dogara ya ce abubuwa sun fi dai-dai-tuwa a lokacin gwamnatin PDP, inda ya zargi jam’iyyar APC da kasa kare rayukan ‘yan Nijeriya da kuma dukiyoyin su.
Post a Comment