Daga Datti Assalafiy
Wani bawan Allah masoyin shugaba Buhari mai suna Hafizu Sufyan yace a isar masa da wannan sakon zuwa ga Baba Buhari, yace Baba Buhari kar ka kalli Zamfara a matsayin wata ‘kasa da ke zaman kanta a constitution, kar ka kalli matsalar gwamnan mu ka dubi matsayin ka a gurin Allah da amanar mutanen jahar.
Lallai ni Hafiz Sufyan kowa ya san masoyin ka ne wanda idan abun bakin ciki ya same ka to idan inada halin hana faruwar shi tun farko zan hana, idan kuma ya faru lallai zan yini cikin bakin ciki. Ina jin nasarar ka nasara ta ce, damuwar ka damuwa ta ce, lallai ina jin dadin na rika ganin ayyukan ka na alheri. Ina jin dadin naga ana yabon ka, ina qin mai kushe ma ka.
Zan tsayu a gaban Allah domin maimaita wadannan maganganu idan karya nake. Ina jin cewa son ka da baka gudun muwa wani bangare ne na addini na saboda kasantuwar ina kyautace maka zato na zama mutumen kirki.
Amma wannan so da nake maka ba zai hana na fada maka gaskiya ba, a gaskiya yana daga cikin abinda ya kara maka nasara a zaben 2015 yawan kisan mutane da ake amma gwamnatin wancan lokaci tayi gummm, ba mai magana.
Haka abinda yake a jahar Zamfara duk da cewa anyi kokari amma abinda yafi damun ‘yan asalin jahar shine yanda kayi shiru akan lamarin baka fitowa kana lallashin su, hasali ma kamar baka san da zaman su ba. Shin ka kyale matsalar ne akan gwamnan mu koko gwamnan ne ya hanaka hubbasa? ko kuwa akwai wata damuwa tsakanin ka da shi gwamna ko kuma ministan tsaro? Duk muna so muji.
Idan wadannan tambayoyin amso shin sune eh to ya kamata ka sanar da mutanen Zamfara da ma ‘yan Najeriya sabida ka samu tsalkakuwa a wani bangare. Son da mu kai maka ba zai zama toshiyar baki ba don yin shiru ga kuskuren ka domin wannan ba shine so ba, domin da mu da kai duk abin tambaya ne a gobe Qiyama inda ba wani sai mai aiki da aikin sa.
Baba Buhari a gaskiya matsalar kisan al’umma matsalar tafi matsalar lalacewar titi, jirgin kasa, gada, matatar man fetur, rijiyoyin man fetur ko gyara kasa, domin duk wadannan ana yin su don mu, shin idan ba mu raye su waye ake yi ma?
Amma wannan ba zai hana kayi kuskure ba don ba daga sama ta 7 ka zo ba, mutum ne kai kamar kowa. Daga cikin abinda ke qara zuzuta wutar zargin ka Zamfarawa keyi na daga cikin kunnen uwar shegu da akayi shekaru masu yawa da yanda gwamnan ke yanda yaga dama a maimakon muga anyi wani abu a’a sai dai muji ance an dankara masa wasu kudade. Yana daga cikin yawace yawace, babban abin takaici irin yanda mu ka ga yayi a zaben nan na fitar da gwani amma shiru ba abinda akai masa na tsawatarwa a matakin Federal.
Har a yanzu bamuga anyi wani abu ba akan wannan zabe ba. Baba Buhari kanada damar fitowa kai muna bayani, kanada damar zuwa ka kawo muna ziyarar jajantawa muji cewa mu ma mutane ne kamar Maiduguri, Kaduna Jos etc. Kanada damar hukunta shi mataki da yawa idan shine matsalar ka. Amma abin mamaki duk da wannan abu sai muji ance yaje gurin ka kuna meeting kuma abinda ya shafi talakawa, ba kaga akwai damuwa??
Wannan kira ne gareka Baba cikin salo na mutuntawa da soyayya ta talaka da shugabann ‘kasa.
Allah Ya baka nasara da lafiya mai amfani Ya maka jagora a duk kudurorin ka na alheri, da abinda zai kawo maslaha ga alummar ka da kasa baki daya.
Allah Ya qarawa rayuwar ka Albarka Ya kuma kawo muna zaman lafiya a Najeriya da duniya baki daya.
Allah kuma Ya baka nasarar lashe zabe mai zuciya cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ameen.
Post a Comment