Daga Yaseer Kallah
A jiya ne ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad, ya yi ikirarin cewa gwamnatinsu ta APC ta cika dukkan alkawuran da ta daukar wa ‘yan Nijeriya.
Ministan wanda ya yi wannan ikirarin ya kuma bayyana wa manema labaran fadar shugaban kasa cewar gwamnatin ta sauke dukkan abubuwan da suka wajabta a kanta, yanzu kuma sai dai kawai dorawa a bisansu idan aka shiga sabuwar shekara.
“Ina taya kowa da kowa murnar bikin Kirsimeti sannan kuma a matsayin gwamnati, muna farin ciki da muka iya cika dukkan alkawuran da muka daukar wa ‘yan Nijeriya tare da sauke abubuwan da suka wajabta a kanmu. Sannan kuma kamar yadda shekara ta zo karshe, mun ayyana kara yin hidima ga ‘yan Nijeriya.”
Post a Comment