Allah ne kadai ya san irin tagomashi da cigaba gami da ‘daukakar da Shugaba Muhammadu Buhari ya ‘kara samu daga wurin al’umma a ciki da wajen ‘kasarnan, sanadiyyar Ihu da neman kaskanta shi da wasu ‘yan jagaliyar ‘yan majalissar tarayya su ka yi masa jiya a zauren hadakar majalissun ‘kasa ya yin da ya ke gabatar musu da kasafin kudin shekara mai zuwa.

Tabbas, duk wanda ya nufi ‘kaskanta Halittar da Allah ya ‘daukaka, ya gamu da wahala, domin ba za ta ‘kaskantu ba, sai dai ma ta ‘kara samun cigaba da ‘daukaka a sanadiyyar hakan, shi kuma mai neman kaskantawar ‘kaikayin da ya watsa sai ya koma kansa.

A jiya aka yi wa Shugaba Buhari wannan rashin arziki, kuma daga jiyan zuwa yau, Allah ne kadai ya san irin mutanen da ada ba sa ‘kaunarsa, wasu kuma sun ‘dan fusata da shi, amma abin da aka yi masan sai ya harzuka su, su ka dawo su fadin sai “Buhari, sai Baba”.

Wasu kuma Allah-Allah su ke duk ‘dan majalissar da ya yi wa Shugaba Buhari ihu, sai ranar zabe in ya je kada ‘kuri’arsa, a mazabar tasa za su ramawa Shugaba Buhari ihun, shi ma ya ‘dan ‘dana ya ji ko da dadi.

Sannan kuma, al’umma da dama, wadanda su na da niyyar zabar Shugaba Buharin, amma kuma ada su na da aniyar zabar wasu ‘yan takara a sauran matakai daban-daban daga wata jam’iyyar, yanzu sun fasa sun ce (APC Sak duk wanda ya ke tare da Buhari shi za su yi), daga sama har ‘kasa babu Mis, domin ba za su sake zabar mutanen da su ka ci zarafin Shugaba Buhari ba, komin kusancin alaka da dangantakar da ke tsakaninsu.

Malam, Lamarin Buhari daga Allah ne.

“Ku mutane ku bar jayayya,
Ku yarda da ikon Allah,
Allah shi ka bai ya ba shi,
Ku zo mu rufa mai baya,
Akwai gaba na nan kuma,
Ba duka za a same sarki ba”.

-Garba Tela Hadejia
Alhamis, 20/12/2018.

Post a Comment

 
Top