Ma’aikatan Majalisar Tarayya da ke yajin aikin kaurace wa gudanar da aikin su, sun bayyana cewa ba za su hana Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ya gabatar da kasafin kudi na 2019 a gaban majalisa ba.
Haka shugaban kungiyar ta su, Bature Mohammed ya bayyana, a yau lokacin da ‘yan sanda suka kafa shingen hana ma’aikatan majalisar shiga ciki.
Mohammed ya ce Buhari ba zai hadu da wani cikas daga ma’aikatan majalisar ba, idan ya zo yau Laraba zai gabatar da kasafin kudi na 2019.
Da safiyar Larabar nan ne ake sa ran Buhari zai gabatar wa majalisa da kasafin kudin a zaman gambiza da majalisar dattawa da ta tarayya za su yi domin sauraren jawabin shugaban kasa din.
Post a Comment