SHARHIN: Bashir Abdullahi El-Bash:-

Duba da yadda lokacin babban zabe na gama-gari ke cigaba da ‘karatowa a Nageria, babu mamaki ga duk wani abu da ya faru ko ya ke shirin faruwa cikin jam’iyyu da Siyasa a Jihar Kano.

Kasancewar Jihar Kano Uwa kuma jagabar Siyasa da yawan magoya baya masu kaunar Shugaba Muhammadu Buhari a Arewa da ma Nageria, ya zama dole a rika kaffa-kaffa kan me zai je ya zo game da Siyasa da zaben shekarar (2019).

Kamar yadda kowa ya sani, a baya-bayannan, labarai sun karade kafofin sadarwa, labaran da ke ayyana aniyar tsohon gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a halin yanzu, Injiya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso na haramar dawowa cikin jam’iyyar (APC), sai dai Sanata Kwankwason ya musanta wannan labari ta bakin hadimansa kan sadarwa irin su Hajiya Binta Spikin.

Duk da haka, wannan labari ba abin aji a kuma dauke masa kai ba ne, dole a dube shi a mahanga ta zahiri, ma’ana, labarin da zai iya faruwa Sanata Kwankwason ya dawo, domin kuwa fara bayyana jita-jitar labarin shiga ko fitar wani ‘dan Siyasa daga wata jam’iyya zuwa wata daga ‘karshe kuma labarin ya tabbata gaskiya, ba sabon abu bane a Nageria, duba da ko fitar Sanata Kwankwason daga (APC) a baya, daga jita-jitar ta fara daga ‘karshe kuma ta tabbata ya fita ya koma (PDP).

Bugu da ‘kari, a yau wasu manyan Fulogan Tafiyar Kwankwasiyyar, irin su Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafeez Abubakar, Alhaji Aminu Dabo, Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa, Janaral Idris Bello Dambazau, Injiniya Mu’azu Magaji, da Alhaji Yahaya Zarewa, sun je fadar Shugaban ‘kasa, Muhammadu Buhari, ya yi musu wankan tsarki irin na Siyasa, lamarin da ake ganin tamkar wata sharar fage su ka yi wa Kwankwason.

Sai dai kamar yadda wasu su ke fadi, Kwankwaso mutum ne da ba ya bi sai dai a bi shi, Kuma wannan ‘dabi’a tasa kusan a iya cewa ita ta hada shi rigima da rashin zaman lafiya tsakaninsa da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma mai girma tsohon gwamnan Jihar Kanon Dakta, Malam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano.

Kamar yadda masu hasashe ke fadi, a yanzu ya zama wajibi ga jam’iyyar (APC) matakin ‘kasa ta yi karatun ta nutsu kan batun dawowar Sanata Kwankwaso cikinta, domin bisa hasashe da nazari, Kwankwaso ba shi da abokan adawar Siyasa da su ka wuci, Gwamna Ganduje, da Malam Shekarau, tunda kuwa haka ne, ‘kila dawowarsa ta zama silar sauya lissafin Siyasa a Jihar.

Tayadda za a iya karbe takarar Sanata daga hannun Malam Ibrahim Shekarau a mayarta gare shi, duba da yadda wasu su ke ganin cewa ai dama har yau babu cikakkiyar alaka da fahimtar juna tsakanin Malam Shekarau da Shugaba Buhari.

Sannan kuma a iya sauya ‘dan takarar gwamnan Jihar, a karbe ta daga hannun Ganduje a kaita inda za a dadadawa Kwankwason.

Wasu kuma na hasashen ai zaman lafiya da ‘dorewar nasarar jam’iyyar (APC) a Jihar Kano, na tattare da wadannan bayin Allah biyu, wato mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma ‘dan takarar Sanata Malam Shekarau, duba da yadda suke wannan tafiya da gaske kuma sun shirya tsaf! Domin ganin Shugaba Buhari da jam’iyyar (APC) sun yi nasara a wannan zabe da ke tafe, sannan al’ummar Jihar Kano masu kada ‘kuri’a su na tare da su ‘dari bisa ‘dari.

Kwankwaso kuwa ana ganin ko da zai dawo din, ba a san da wacce zai zo ba, duk kuwa da cewar shi ma na da nasa dimbin mabiyan da sanin harkallar Siyasa ciki da bai, shin neman mafita da masalahar kowa ko kuwa neman kamun makamar yi wa Shugaba Buhari da jam’iyyar (APC) ‘kafar Ungulu ce za ta kawo shi ?

Yanzu dai a iya cewa kallon ya koma sama, abin jira kuma a gani, shi ne ko Kwankwason zai biyo wadancan Fulogai nasa, kuma mai zai faru cikin Siyasar Kano, idan ya dawo ‘din, ko Jam’iyya za ta sauya manyan abokan adawar Kwankwaso a Siyasa domin dadada masa, ko kuwa za ta kauda kai ta kalli masalaharta shi ma Kwankwaso ya hakura ya zama ‘dan bi daga bisani a saka masa da wasu abubuwan ?.

Duk amsoshin wadannan tambayoyi, lokaci ne kadai zai bayyanasu

Bashir Abdullahi Elbash,
Shugaban Cibiyar Sabuwar Kafar Sadarwar Zamani, Ta Shugaban Nageria Muhammadu Buhari, (BNMC) Na Jihar Kano
Alhamis, 20 ga watan Disamba, 2018.

Post a Comment

 
Top