Daga Datti Assalafiy
Ba’ayi sati guda ba an tare motocin matafiya akan hanya har guda hudu a jihar Zamfara akayi garkuwa da mutanen cikin motocin gaba dayansu
Jiya Lahadi akwai motar ‘yan agaji Izala an taresu anyi garkuwa dasu a hanyar Zamfara gaba dayansu kuma ance yawansu yakai mutum ashirin kamar yadda jaridar Rariya ta wallafa labarin
Kuma duk inda wani ‘dan Zamfara yake zakaji yana batun mawuyacin halin da jihar ta fada ciki a dalilin masu sace mutane
Wasu bayin Allah da basu jima da bin shafi Datti Assalafiy ba sunce wai naki yin magana akan abinda yake faruwa a Zamfara, amma wadanda suke tare dani watanni uku da suka gabata sunga irin rubutun da nayi akan abinda yake faruwa a Zamfara
Amma har ga Allah a yanzu zaiyi wahala na kara cewa komai akan Zamfara, saboda na gamsu da shawaran da aminai na irinsu Ahmad suka bani.
Wallahi a Nigerian nan muna cikin wani yanayi da idan dai zaka fito ka bada shawara ga mahukunta wanda an tabbatar idan akayi amfani da shawaran za’a samu mafita to kai da ka bada shawaran za’aji haushinka, za’a bibiyeka da sharri ta ko’ina, musamman idan abinda yake faruwa akwai hannu wasu kebantattun mutane a ciki
Idan zaku tuna anan har rubutu nayi nace ina son na samu hanyar da zan gana da shugaba Buhari a sirrance, mu tattauna akan tsaro, akwai boyayyun mutane masana sirrin tsaro ‘yan baiwa da zan fadawa shugaba Buhari cewa ya nemesu, to wannan sanarwa da na fitar maciya amana basu so ba, saboda akwai sanayya tsakaninmu “kar ta san kar!”
Dole zamu hakura don mu tsira, kuma fadan da yafi karfinka akace sai ka mayar dashi wasa, indai kana zaune a Nigeria ganganci da rayuwa ne kace zaka bayyana gazawar wasu masu ikon tsaro, burinsu kawai shine a bayyana kokarinsu ko da ya tabbata cewa sun gaza, imba haka ba za’a ma sharri ace ka kai matsayin babban kwamandan Boko Haram don a dakile ka
Wannan shine halin da muke ciki, kuma wannan shine abinda yake faruwa, shiyasa kukaga masana sirrin tsaron Nigeria da shugabanninmu na arewa da manyan sarakunanmu kowa yayi shiru ya kame bakinsa akan abinda yake faruwa a Zamfara da jihar Borno saboda neman tsira daga sharrin maciya amana
Amanar shugaba Buhari akeci, kuma idan har wannan gwamnati tamu mai albarka bataci jihar Zamfara a zaben 2019 ba to kar kowa yaga laifin mutanen Zamfara, saboda har ga Allah babu abinda wannan gwamnatin tamu zatayi kanfe dashi a jihar Zamfara tunda an gaza wajen karesu daga sharrin masu sace mutane
Muna rokon Babban Sarki Allah Buwayi Gagara Misali Mai iko akan komai da kowa Ya kawo daukinSa a jihar Zamfara
Post a Comment