ZABEN FIDDA GWANI:
Ranar 2 ga Oktoba 2018, jam’iyyar PDP ta kasa karkashin Cif Uche Secondus ta aiko kwamitin zabe don ya sa ido ya kuma gabatar da zaben dan takarar gwamna na PDP.

Shugaban kwamitin riko na PDP na jiha Rabi’u Sulaiman Bichi ya shirya gudanar da zaben a sinimar Marhaba, amma jami’an ‘yan sanda suka hana. Sun dogara da dalilan cewa Mas’udu Doguwa shi ne halastaccen shugaba. Da Salihu Sagir Takai da Abba K Yusuf da Sadiq Wali da Ja’afar Sani Bello da Akilu Sani Indabawa da Ibrahim al Amin Little duk sun sayi fom na takarar kuma jam’iyya ta tantance su a Kaduna ta basu izinin su shiga zabe.

A lokacin da ‘yan sanda suka hana gudanar da zaben a Marhaba, cikin dare kwamitin kasa na zaben yaje gidan tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ke Lugard ya aiwatar da zaben. Da Abba K Yusuf da Jafar Sani Bello sune suka shiga zaben, sauran suka kaurace kuma aka bada sanarwar nasarar Abba K Yusuf da kuri’a 2,421, Ja’afar Sani Bello yazo na biyu da kuri’a 1,258, sai kuma Takai da bai shiga ba aka bashi 410. Jam’ian da suka wakilci jam’iyya da hukumar zabe ta INEC suka bada rahoton an yi zabe ga yadda sakamako ya kasance.

DAWOWAR ABBA K YUSUF PDP

A bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP duk wanda ya fita daga cikinta, kamar shi Abban Kanawa, in yana son sake dawowa sai ya rubuta takarda zuwa ga sakataren jam’iya na mazaba, kamar shi Abba zai kai tasa takardar ne da hannunsa gurin sakataren mazaba, wacce a ciki zai yi bayanin yana son dawowa. Sannan a karbe shi. Duka wannan tsarin Abba bai yi shi ba, a bisa tarin hujjoji da aka baiwa kotu.

A lokacin da Abba ya lashe zabe a Lugard ba shi da katin kasancewa dan jam’iyyar PDP. Babu sunansa a rijistar PDP. Ita rijistar ma an rigaya an rufe shigar da sunan kowa, a bisa dokokin jam’iyya. Sakataren mazabar Diso ya tabbatar da haka.

KORAFIN JAFAR SANI BELLO
Jaafar Sani Bello ya kai kara gaban alkali A.T Badamasi yana korafi akan cewa, jam’iyyar PDP ta bada takara ga wanda ba danta ba, don haka yana rokon a cire sunan Abba K Yusuf a gurbin a mayar da nasa sunan. Akan wannan an yi zama sau hudu, suna lauyan Jafar Sani Bello Barista Abdul Fagge, lauyan Abba kuma Adeboyega Awomolo SAN.

SAKATAREN PDP NA MAZABAR DISO

Da kotu ta fara zama, shari’a ta fara kankama, sai sakataren jam’iyyar PDP na mazabar Diso, inda Abba ya fito, ya yi baki biyu, wato ya sauya magana. Da farko ya ce Abba ba dan jam’iyya bane, daga baya kuma ya ce Abba ya dade da mika masa takarda ta neman shiga PDP kuma ya karba. Wannan abin ya sabawa rantsuwar kotu da sakatare ya yi. Ganin yana shirin yin wasa da shari’a Ja’afar Sani Bello ya maka shi gaban kotun majistare bayan ‘yan sanda sun tuhume shi da laifin fojare da karya da boye shaida.

YADDA SHARI’AR TA GUDANA
A matsayinsa na wanda ya shigar da kara, Ja’afar Sani Bello ya mika hujjojinsa, ya gabatar da shaidunsa, kuma kotu ta karba. Shima Abba a matsayinsa na mai kariya, ya bada hujjojinsa na kare kai, da shaidunsa kuma an karba, bayan doguwar muhawara a tsakanin lauyoyi a ranar Talata da ta gabata. Duka lauyoyin sun tabbatar da abubuwan da suka rubuta, sun yi wa kotu jawabin karshe. Alkali A.T Badamasi na kotu mai lamba ta uku a Babbar kotun jihar Kano, wanda ya shahara da bin ka’ida da aiki da hujja da rashin tsoro da rashin son zuciya da kamanta gaskiya ya bada ranar 14 ga Janairu 2019 cewa zai yanke hukunci.

YADDA HUKUNCI ZAI KASANCE
Ranar da za a yanke wannan hukunci saura kwana 31 a yi zaben shugaban kasa da majalisar dattijai da tarayya. A kuma wannan ranar ce INEC zata fitar da sunaye cikakku na karshe na duk ‘yan takara. Abin da babu makawa zai faru shi ne ko dai a kori wannan shari’a, Jafar Sani Bello ya karbi kaddara, ya hakura ko ya daukaka kara. Ko kuma kotu ta amsa rokon Jafar ta tabbatar da rashin gaskiyar Abba, sannan ta umarci INEC ta zare sunan Abba ta mayar da na Ja’afar Sani Bello a madadinsa.

IDAN JAFAR YA YI NASARA
A yadda na bibiyi wannan shari’a, in har Jafar ya yi nasara akan Abba, za a maimaita irin abin da ya faru a tsakanin Mohammed Abacha da Jafaru Isa a jam’iyyar CPC a shekarar 2011.

Idan kotu ta baiwa Jafar nasara tare da umarnin INEC ta sanya sunansa PDP ta fada mafi girman rikici na rashin tabbas din dan takara. Yadda ake da sabani a tsakanin Jafar Sani Bello da mai gidan Abba, wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba zasu amince da wannan nasara ba. Zasu daukaka kara, lauyan Abba kwararre ne kuma Kwankwaso yana da nacin shari’a.

Abu na biyu, jam’iyyar PDP ta Kano kashi 98 yana hannun ‘yan Kwankwasiyya, kashi biyu yana hannun mutanen Aminu Wali da Akilu Indabawa dukkansu basa shiri da Ja’afar, ko sun karbi hukuncin ba zasu yi aiki tare da shi ba.

Na uku idan Abban Kwankwasiya ya karbi wannan hukuncin, sai dai su hada kai da sauran ‘yan PRP da kananan jam’iyyu a bayan Salihu Takai don yakar abokin fadansu na zahiri kuma na gaske gwamna Ganduje, amma fa ina ganin akwai wahala matuka a samu fahimtar da ‘yan Kwankwsiyya za su bi PRP, su yi aiki tare bayan Kwankwaso da kansa ya ce “Mayen gwamna baya gwamna” kuma an rufe kofar sauya sunan kowa a kowane mataki na takara, sannan ga kwantaccen sabanin da aka samu da juna.

Idan kun lura kuma yanayin jagororin da suke fita daga tsarin Kwankwaso saboda huce haushinsu basa tafiya PRP ko wata karamar jam’iyya, sun fi karkata zuwa APC. A gaskiyar magana in an baiwa Jafar nasara a kotu tsuguno bata kare masa ba, sabon rikici ne zai barke. Ba tantama za a kashe gwiwa da karsashin Kwankwasiyya amma ba zasu taba bari Ja’afar ya zauna lafiya ba. Za a jika masa aiki.

Ja’afar Sani Bello zakakuri ne shima kuma in an ba shi, sai ya tashi haikan wajen nemo mataimakin da zai rufa masa baya da tsara wadanda zasu rike masa amanar zabe da tsara yadda zai yi kamfen da daidaita sabaninsa na Kano dana kasa da gina mu’amala da dan takarar shugaban kasa na PDP da sanatoci da ‘yan refs da na majalisun jiha, duka wannan a cikin sati bakwai, don shi ne kawai lokacin da yake da shi. A takaice a fahimtata nasarar Jaafar a wannan shari’a kassara tsarin Kwankwasiyya ne, amma babbar nasarar kuma ta Ganduje ce.

IN AN BAIWA ABBA NASARA
Kotu ta baiwa Abba nasara ba sabon labari bane. Zai ci gaba a gwadaben da yake kai, Abba ya tsallake rijiya ne kawai da baya, sannan an dada karfafafa tsagin Kwankwasiyya na PDP a Kano. Wadanda suka rika yi wa Kwankwasiyya zagon kasa ko shagube su shiga taitayinsu.

Wannan sharhi ne kawai da fahimtata amma Allah Ta’ala shi ne kadai mafi sani.

Post a Comment

 
Top