Uba ya kashe ‘yarsa a Kano

Wani mahaifi mai suna Sani Lawan Kofar Gabas a karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano ya kashe ‘yarsa mai shekara Uku a duniya bisa ta dameshi kuka.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, SP. Magaji Musa ne ya bayyana wa manema Labaru hakan a jiya Litinin a Kano.

Majiyarmu ta ‘Kano Today’ ta ruwaito cewa mahaifin yarinyar ya yi sanadin mutuwar yarinyar ne ta bata gubar Fiya-Fiya da yayi ta sha.

Lawan Kofar Gabas ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fusata da ita ne yayin da ta ishehsi da kuka saboda wani ciwo da ta ji a kafarta.

Kakikin ‘yan sandan jihar Kano, ya ce karamar yarinyar ta fara amai baya da aka bata gubar, inda mahaifin da kaninsa suka yi gaggawar kai ta asibiti amma daga bisa ‘yar ta mutu tun kafin likitoci su kai ga tabata.

Magaji Musa ya ce nan ba da jimawa za su mika mahaifin yarinyar ga kotu domin ya karbi hukunci daidai da abin da ya aikata.

Kakan yarinyar Malam Saminu Sulaiman wanda ya yi magana a madadin iyalan yarinyar, ya ce za su tabbatar da mahaifinta ya fuskanci hukuncin kashe ‘yarsa da ya yi.

Post a Comment

 
Top