A yayin da hayaniyar siyasa ta dau zafi bari mu dan shakata da wannan*

1. Idan Mace na wahalar da Namiji sai ace kawai sake ta auro wata. Amma idan Namiji na wahalar da Mace sai ace ta yi hakuri Aljannar ta na Karkashin kafar mijinta.

2. Mace ta yaye tsiraicinta saboda rashin tsoron tsinuwar Allah amma ta rufe tsiraicinta saboda tsoron sanyi.

3. Namiji ya gama yawon neman matan banza a waje, amma idan ya zo aure ya ce Ustaziya ya ke son aura.

4. Mace ta fifita biki akan ba wa mijinta cikakkiyar kulawa idan ya so kara aure ya zama Namiji Dan kunama.

5. Maza su zauna a majalisa suna fadin ‘ya’yan unguwa wance da wance sun lalace amma idan dare ya yi sune abokan shakatawarsu.

6. Mace ta gama yabon ‘yar makota ‘ga hankali ga tarbiyya amma ba mijin aure abin tausayi ga ta marainiya’. Da Namiji ya so aurenta ya zama mara amana.

7. Namiji ya kashe kudade a wajen cin abinci yana fadin ‘Da yadda mata suka iya makeup haka suka iya girki da mun ji dadi’ amma ya bar gida da miyar kuka.

8. Mace ta gama zagin Uwar Miji, amma idan ta haifi da matarsa ta mallake shi tace bata yarda ba asiri ta yi masa.

9. Namiji ya auri Mace tagari ka gan shi ya tare a otal da ‘yar bariki, idan ka tambaye shi ya ce ba ta iya soyayya ba. Idan ance ya auri wannan ya ce ‘yar iska ce.

10. Mace ta rika kwana da mazan wasu a otal amma tana fadin idan ta yi aure ta kama mijinta da wata kashe ta zata yi.

11. Namiji ya yi shekara da shekaru yana bin gidan Budurwa ayi da shi ya fito yace bai shirya ba, amma idan ya gan ka wajen kanwar sa yana cewa ka fito ka ce ba ka shirya ba, zai yi maganin ka.

12. Mace ta ce da kishiyar gida gara ta waje amma idan ta haifi mace so ta ke yi a aure ta.

13. Namiji ya rika ihun Soyayya sai su Kareena amma a Gida ya kasa zama Sharukhan.

14. Mace ta tsangwami Mijinta da zagi da gori ya kasa tsinana mata komai a rayuwa, ‘in banda kaddara me zai sa na aure ka? Amma da ya fadi ya rasu sai ihun yanzu yaya zan yi ya mutu ya bar ni da ya’ya?

15. Namiji ya dage Mace fara ko mayya ce, amma ya cika sohiyal midiya da ihun Mata sun lalace da bilicin.

16. Namiji na cikin bakin talauci ci da kyar sha da kyar ba kudin kai yara makaranta, amma Mace na addu’ar gara su zauna a talauci da ya samu arzikin kara aure.

Allah Ya sa ban fifita wani sashi akan wani ba.

Post a Comment

 
Top