Daga Datti Assalafiy
Rundinar kwararrun ‘yan sanda na IGP Intelligence Response Team (IRT) karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun samu nasaran cafke kasurgumin kwamandan Boko Haram mai matukar hatsari wanda ake nema ruwa a jallo, an cafkeshi a maboyarsa dake jihar Lagos.
Sunansa Umar Abdulmalik, shine wanda ya tsara ya kuma jagoranci mafi munin harin bomb a Kuje da kasuwar Nyanya a Abuja a shekarar 2015 inda mutane kusan 200 suka hallaka nan take.
Sannan shine wanda ya jagoranci kaddamar da harin ta’addanci a guraren duba ababen hawa na ‘yan sanda dake shatalelen Galadimawa a birnin Abuja wanda yayi sanadiyyar hallaka ‘yan sanda 7 da suke bakin aiki, sannan shine ya kaddamar da hari a Lugbe da Gwagwalada wanda ya lakume rayukan ‘yan sanda duka a Abuja.
Har ila yau wannan rikakken ‘dan Boko Haram shine ya jagoranci kaddamar da fashi da makami a wasu bankuna dake jihar Edo da Ondo da wasu kashe-kashen da akayi a Okene jihar Kogi, sannan shine babban kwamandan da ya jagoranci fasa kurkukun jihar Niger a farkon wannan shekara inda yayi sanadiyyar kubutar da ‘yan gidan yari sama da mutum 100, a wannan harin ne ya rasa idonsa guda daya.
An samu nasaran cafkeshi ne a jiya alhamis a dalilin wasu yaranshi hudu da aka kama a Abuja aka samu bindiga kirar AK47 guda hudu da harsashin bindiga masu yawa amma shi ya samu nasaran tsallekewa harin da ‘yan sanda suka kaddamar masa ya gudu zuwa Lagos tare da raunin harbin bindiga a jikinsa, jami’an ‘yan sanda da suke aiki karkashin DCP Abba Kyari sukabi diddiginsa aka kamashi jiya.
Hakika wannan nasarace mai girma daga Allah (SWT), domin rayuwar rikakkun ‘yan Boko haram irin wannan a cikin al’umma abune mai matukar hatsarin gaske.
Tabbas DCP Abba Kyari ajiyar Allah ne, mu dai ‘yan Nigeria bamu da abinda zamu sakawa Maigirma shugaban ‘yan sanda IGP Ibrahim K. Idris da babban yaronsa DCP Abba Kyari face addu’ah da fatan Allah Ya kara masu taimako da nasara da tsaro.
Post a Comment