Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ƴan Najeriya da su hada hannu wajen yaƙar matsalar rashin tsaro da mulkin son rai a ƙasar nan, Obasanjo ya faɗi hakan ne a wajen bikin cikar Farfesa Ango Abdullahi tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaraiya shekaru 80 da haihuwa wanda aka gudanar ya tilas ne matsalar rashin tsaro a ƙasar nan ke ƙara tabarbarewa.

Kuma Obasanjo ya ce sam bai kamata dattawan ƙasar nan su zura ido akan abin da ke faruwa a halin yanzun ba, yin hakan daidai yake da shuka matsalar wargajewar ƙasar nan, Ba wanda ya isa ya ji cewa zai iya mallakan ƙasar nan a rigimance, matukar kuwa aka kai mutum bango a irin hakan matukar ƙasar mu ba a daidai take tafiya ba, to kuwa ya hau kanku, ƴaƴan mu, matasa da mu iyayenku ba maganan shekaru a nan, da mu hada hannu mu yi aiki tare wajen mayar da ƙasar mu a kan hanya madaidaiciya ba wanda ya isa ya ce, kasata ce ni kadai, don haka zan yi duk yanda na so, Allah ba zai bari hakan ya faru ba.

Post a Comment

 
Top