Daga Yaseer Kallah
A yunkurinsa na ya sanya ‘yan majalisar da ke masa ihu su nutsu a lokacin da yake gabatar masu da kasafin kudin 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce masu “duniya dai tana gani.”
Ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba ‘yan majalisar suka dinga katse hanzarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da sowa da ihu a sa’ilin da yake gabatar masu da kasafin kudin. A lokacin da Shugaban kasa ya soma karanto nasarorin da gwamnatinsa ta samu sai fusatattun ‘yan majalisar suka soma yi masa ihun Karyane! Ba Haka Ba Ne! Barawo! da sauran kalaman diban albarka da rashin mutunci.
Amma da Shugaba Muhammadu Buhari zai maida masu martani sai ya ce, “Shin na iya tuna wa ‘yan majalisar tarayya cewar duniya tana kallonmu. Ya kyautu a ce mun girmi haka.”
Tuni martanin da shugaban kasa ya mayar tare da kamun kan da ya nuna ya sanya sauran ‘yan majalisar suka hau yi masa tafi, raf! raf!! raf!!!
Post a Comment