A kalla mutane 3,252 ne ‘yan jam’iyar adawa ta PDP da suka koma jam’iyar APC daga mazabar Sanata Dino Melaya ta Kogi ta Yamma a jihar Kogi.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito a jiya cewa, daga cikin masu sauyin shekar akwai tsoffin kwamishinoni Biyu, na albarkatun ruwa, Mista Tunji Oshanusi da na Gona, Femi Abolarinwa.
Shugaban jam’iyar APC mai kula da shiyar Kogi ta Yamma Hon. Ropo Asagun ne ya karbi tsoffin ‘yan jam’iyar PDPn a babbar dandalin wasa da ke Kabba, a yayin taron kaddamar da yakin neman zaben shiyar.
Asagun ya yabawa masu sauya shekar bisa shawararsu na dawowa jam’iyar mai mulki, inda ya ce hakan na nuni da cewa jam’iyar APC ta taka yi abin a zo a gani tun daga matakin jiha zuwa ga tarayya.
A nashi bangaren, kakakin majalisar jihar Kogi, Cif Mathew Kolawole, ya bukaci jama’an da su gaggauta karbar katin zabe mai zaman kansa domin zaban APC.
A cewar Kolawole, “jam’iya APC ce kadai jam’iyar da za ta iya cetomu daga hannun masu wawure kudin kasa; dan haka kar ku yadda ku sayar da ‘yancin ku, kuri’ar ce ‘yancinku”.
Ya kara da bayyana musu cewa, “a cikin shekaru Uku da rabi, shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa sun yi abin yabawa”. Inji kakakin majalisar.
Shi ma tsohon shugaban kamfanin jaridar Daily Trust, Misata Ishaq Ajibola ya bayyana cewa al’uman Yagba sun amfana kwarai da samun manyan mukaman siyasa da kuma aiyukan raya kasa daga gwamnatin jiha.
Ya roki al’uman yankin da su zabi jam’iyar APC a zabe mai zuwa domin ci gaba da morar romon Dimokaradiyya.
Da yake jaddada kudirinsa ga yankin idan aka zabeahi, dan takaran Sanata a mazabar Kogi ta yamma Sanata Smart Adeyemi, ya yi alkawarin yin jagoranci ta gari ga al’umar yankin.
Smart, ya bayyana cewa shugaban kasa na iya bakin kokarinsa domin ci gaban kasar nan inda daga ciki ya ce ya na kokarin ganin masarrafar karafuna ta Ajaokuta ta fara aiki nan ba da jimawa ba, sannan shimfida Layin dogo a kar nan da zai ya fita ta
Post a Comment