Daga Haji Shehu
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) reshen jihar Enugu ta kama wasu makudan kudade a filin tashi da saukan Jiragen sama na Akanu Ibiam dake jihar Enugu.
Kudin wanda suka kai Dalar Amurka Miliyon $2.8m, daidai da Naira Biliyon N1.02bn a cikin wasu akwatuna guda biyu anyi ram dasu ne a daidai lokacin da ake kokarin tsallakawa dasu zuwa jihar Lagos.
Mutanen masu suna Ighoh Augustine da Ezekwe Emmanuel, suna aikine wa wasu Kamfanoni, Mai aikatan Banki, wajen karkatar da akalar haramtattun kudade. Da suke amsa tambayoyi daga hukumar EFCC, mutanen sun shaida cewar sun kai Sama da shekaru 6 suna wanga mummunar aika-aika
Post a Comment