Daga Sale Kura

MUSULMI YA ZIYARCI COCI BA LAIFI BA NE..

Shi Musulmi a koda yaushe mutum ne mai saukin kai da fahimta, babu tsanani, ko takura a cikin addini, balle har hakan ya kai ga samun busassun zukata da daskararrun dabi’u!.. Addini ne na sauki, da tausayi da jinkai ((Lallai saboda rahamar da ta zo maka daga Allah ne ka zamo mai saukin kai a tare da su, da a ce za ka zamo mai tsanani da kekashewar zuciya da sun fashe sun barka..)) (Ali Imran : 159).

Maganganun da wasu masu tsattsauran ra’ayi suke yawan yadawa, na kyamatar wadanda ba Musulmi ba, abu ne da ba shi da dangantaka da karantarwar Musulunci, suna dai fadin abin da ya yi daidai da zukatansu ne, wadanda da ma babu wani wuri na rahama da jinkai a cikin su, kuma mun sani cewa, sai dai tausayi da jinkai ne ake samun kyakkyawar rayuwa ta zamantakewa da addinin Musulunci ya wajabta wa duk wani Musulmi na kirki kan ya nuna, a yayin da rayuwa ta hada shi da wanda ba Musulmi ba..

Saboda haka, a nan zan kawo labarin Kiristocin Najran da suka ziyarci Sayyiduna Rasulullahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a Masallacin sa, da kuma irin tarbar da ya yi masu, ta kai har sun sami sarari na yin ibadar su a cikin Masallacinsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ..

Bayan sa kuma zan kawo ziyarar da Sayyiduna Umar Bn al-Khaddab (Allah ya kara yarda da shi) ya kai Cocin al-Kiyama a garin Kudus..

Zan kawo wadannan matsaya guda biyu ne, domin masu karatu su fahimci irin wancan muguwar fahimta, ta yada gaba da kiyayya -da sunan addini – da wasu suke dakonta babu gaira babu dalili, ga su kaman haka :

1- KIRISTOCIN NAJRAN SUN ZIYARCI ANNABI A MASALLACIN SA:

Malaman Tarihi da Sirah sun bayyana cewa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya sauke tawagar Kiristocin da suka kawo masa ziyara daga garin Najran a Masallacin sa, ya kuma ba su dama, na su yi ibadarsu a cikin Masallacin sa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); Ibn Kasir yana cewa : Ibn Ishaq ya ce : Muhammad Bn Ja’afar Bn az-Zubair ya ba mu labari cewa : Sun zo wurin Manzon Allah a garin Madina, sai suka shiga cikin Masallacin sa lokacin sallar La’asar, suna sanye da tufafi na Kittani da aka yi masa ado irin yanda Bani Al -Haris Bn Ka’ab suke yi, sai mai ruwayar Hadisin ya ce : Sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da suka gan su suna cewa : ba mu sake ganin wata tawaga irin tasu ba, da lokacin ibadar su ya yi, sai suka mike a Masallacin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) suka fara sallar su (ibadarsu), sai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce : ((Ku kyale su)) suka yi sallar su suna fuskantar yankin gabas.. ‹‹Duba: Tafsirul Kur’anil Azeem, 2/42, darul kutubul ilmiyya››.

Haka ma Ibn Kayyim al-Jauziyya ya fadi a cikin littafin sa «Ahkamu Ahluz zimmah, 1/397» cewa : Hadisi ya inganta daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa : ya sauke tawagar Kiristocin garin Najran a Masallacin sa, da lokacin sallar su ya yi, sun yi sallar su a cikin sa, wannan kuwa ya faru ne a Amul wufud.. Haka ma ya kawo irin Hadisin da Ibn Kasir ya fadi a cikin littafin «Zadul Ma’ad fi Hadyi Khairil Ibad, 3/549»…

2- SAYYIDUNA UMAR YA ZIYARCI KIRISTOCIN KUDUS A COCIN ALKIYAMA :

Bayan bude kasar Palastine a shekara ta 16 bayan hijirar sayyiduna Rasulullahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sayyiduna Umar Bn al-Khaddab (Allah ya kara yarda da shi) ya yi tafiyayyiya zuwa birnin Kudus, domin ya amshi mabudin garin kaman yanda Sojojin Musulmai suka cin ma yarjejeniya da Kiristocin da suke a garin..

Babban Pada na al-Kudus “Safruniyus”, wanda shi ne ya jagoranci rubuta wannan yarjejeniyar ta bangaren Kiristoci ya gayyaci Halifa Umar (Allah ya kara yarda da shi) zuwa Cocin “al-Kiyãma” [Cocin da aka haifi Sayyiduna Isah (AlaiHis salam) a ciki], ya kuma amsa wannan gayyata, ya kuma tafi, har lokacin sallah ta riske shi a wurin, sai ya nemi a nuna masa wurin da zai yi sallah, sai Babban Pada na al-Kudus “Safruniyus” ya nuna masa cewa zai iya yi a ko’ina a cikin Cocin, sai Sayyiduna Umar (Allah ya kara yarda da shi) ya ce masa: “A’a ba za a yi haka ba, bai kamata Umar ya yi Salalh a cikin Cocinku ba, gudun kada Musulmai daga baya su zo su ce : a nan Umar ya yi sallah, don haka za su gina Masallaci a wurin!!”, haka ya sanya ya fita daga wajen Cocin ya yi sallarsa.. Daga baya an gina Masallacin a wurin akan sanya masa suna : “Masallacin Umar”…

Wadannan labarai guda biyu da na farko ziyarar Kiristoci zuwa Masallacin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), na biyun kuma ziyarar Halifa Umar Bn al-Khaddab (Allah ya kara yarda da shi), sun isa su zama hujja..

Ina fatan za a dawo a sallama wa dalili, a kuma nesanci yi wa Allah karan – tsaye..

Allah ya ganar da mu baki daya..

Saleh Kaura

(C) TASKAR SUNNA

Post a Comment

 
Top