Daga Datti Assalafiy
Jama’a ku kara fahimtar halin da muke ciki, da kuma wadanda suke da hannu wajen karfafa ayyukan ta’addanci a Nigeria, jiya Lahadi shahararren tsohon Taraba tsohon shugaban sojoji kuma tsohon ministan tsaro wanda watannin baya ya fito a filin Allah ya zargi rundinar sojin Nigeria da hannu wajen haifar da rikicin fulani makiyaya da manoma sannan yayi kira ga ‘yan uwanshi da su dauki makaman yaki su kare kansu, a dalilin zargin sai da shugaban sojoji Laftanar Janar Buratai ya mayar masa da zazzafan raddi.
To a jiya Lahadi 23-12-2018 tsohon ya halarci wani taro kan addininsu na nasara da aka gudanar a wani katafaren dakin bautarsu dake birnin Abuja, sun hadu akan taron da suka saba gudanarwa a karo na sha daya (11th Festival of Praise) taken taron nasu shine “Sing out! Our God reigns”, an bawa tsohon dama don yayi jawabi, farkon abinda ya fara furtawa a bakinshi shine “Nigeria tana tsakiyar yaki”, yace duk rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adama na duniya (Amnesty International) ta fitar akan sojojin Nigeria gaskiya ne, yanzu ko’ina yaki ake a Nigeria.
Tsohon yacigaba da cewa wannan yaki gaba daya ya shafemu, ana yakarmu, gwamnatin Buhari ce take yakarmu, rahoton Kungiyar kare hakkin bil’adama gaskiya ne, ina kira gareku gaba daya kuje ku nemi cikakken rahoton ku karanta, abinda wadannan turawa suka fada mana a rahotonsu duka gaskiya ne, ya zama wajibi a garemu mu tashi tsaye don samarwa kanmu mafita.. a cewarsa.
Jama’a kun dai ji daga bakin tsoho, kuma abinda nakeso ku sani shine wannan tsohon shine yake lura da ayyukan wadannan kungiyoyin kare hakkin bil’adama a arewa maso gabashin Nigeria, duk tallafin da zasu bayar sai da saninshi, dukkan tsare tsaren ayyukansu na fili da na sirri yana da masaniya a kai, hatta yadda suke tallafawa ‘yan ta’adda da wadanda suke baiwa kungiyoyin umarni kan yadda zasu tallafawa ‘yan ta’adda yana da masaniya a kai, kuma matukar wannan tsohon yana nan a Nigeria da kamar wahala a kawo karshen ayyukan ta’addanci domin sune manyan masu tsara yadda za’a karfafi ta’addancin a Nigeria suna fakewa da kariyar addini.
Saboda haka kar kowa yayi mamaki don wannan tsoho ya fito ya goyi bayan rahoton karya na wadannan kungiyoyin sharri da suka mamaye jihar Borno, tare dasu yake aiki, bakinsu daya, don haka kowa ya fahimci suwaye makiya zaman lafiyar Nigeria da wadanda suke daukar nauyin kwangilar ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashin Nigeria.
A kullun burina shine masu karanta sakona su fahimci illar rahoton da wadannan kungiyoyin sharri suke fitarwa, babban manufar hakan shine a hana gwamnatin Nigeria sayen manyan kayan yaki na zamani wanda zasu taimaka a yaki ayyukan ta’addanci, saboda kamar yadda ministan Tsaro Malam Mansur Dan Ali ya bayyana kungiyoyin sharrin basa kaunar a gama da ayyukan ta’addanci a Nigeria saboda ta hakane suke samun makudan kudaden shigarsu, shiyasa suke tallafawa kungiyoyin ta’addancin domin su cigaba da wanzuwa a kasarmu Nigeria.
Akwai rabutuna da yake tafe insha Allah mai taken SU WAYE BASA KAUNAR NIGERIA TA ZAUNA LAFIYA TSAKANIN SOJOJIN NIGERIA DA KUNGIYOYIN SHARRI kada kowa ya bari a bashi labari.
Allah Ka mana maganin makiya zaman lafiyar mu
Post a Comment