Daga Amina Yusif Ali

Bayan ɗaukar dogon lokaci ba tare da ya ce komai ba, Shugaban ƙasar nan Muhammadu Buhari ya mai da Martani ga ikirarin da Matarsa Kuma First Lady, Aisha Buhari ta yi. A yayin zantawarsa da sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka (VOA ).

Shugaban ya bayyana cewa ikirarin da mutane suke yi na cewa akwai wasu mutane guda biyu da suke juya shi wajen gudanar da mulki duk zuƙi-ta -malle ce. Hasali ma, ta ƙara nuna cewa shi cikakken ɗan siyasa ne. Sannan kuma ya ƙalubalanci masu yi masa irin wannan zargi da su kawo masa hujja guda ɗaya tak da take nuna Wani abu kwaya ɗaya da waɗancan mutanen da ake zargin suna juya shi suka tilasta masa ya yi.

Tambayar da VOA ta yi masa ita ce; “me za ka iya cewa game da abinda mutane suke faɗa cewa wasu mutane ƙalilan da ake zargin su ne ‘fulogan’ da suke tafiyar da mulkin ƙasar nan ta bayan fage? ko a kwanan nan ma matarka ta yi jawabi a kan hakan”.

Buhari ya amsa da cewa; “wannan kuma matsalarta ce, ita ya shafa. Kuma hakan ya nuna cewa ni cikakken ɗan siyasa ne. Domin abinda suke faɗa ya sha ban-ban da yadda abin yake a zahiri. Don haka ni ma ina ƙalubalantarsu da su zo su faɗi abu guda daya da waɗancan ‘fulogan’ suka tilasta min na aikata. Idan mai karatu bai manta ba, a kwanakin baya Uwargidan shugaban ta bayyana cewa akwai wasu mutane guda biyu da suke juya Buhari wajen tafiyar da mulkin ƙasar nan.

Wannan furuci na Aisha Buhari ya yi matuƙar yamutsa hazo irin na siyasa a ƙasar nan. Inda ‘ƴan ɓangaren adawa da Buhari suka yi ta tofa albarkacin bakunansu.

Post a Comment

 
Top