BABU MAI HANKALIN DA ZAI YARDA DA MAYAUDARA MA’INTA
Daga Datti Assalafiy
a karanta raddin da Atiku Abubakar yayi wa shugaba Buhari a shafinsa na facebook saboda wai shugaba Buhari bai halarci jana’izar sojojin Nigeria da suka rasa rayukansu a harin Metele ba.
Kafin nace wani abu ina so na kara tunatar da ‘yan Nigeria cewa lallai akwai boyayyen tsarin da jam’iyyar PDP tayi domin tayi amfani da tsarin wajen yaudarar ‘yan Nigeria a karo na biyu.
Tsarin kuwa shine; sunce duk wata matsala ta barazanar tsaro da ta faru a cikin ‘kasa, wanda ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga sukaci nasara, to ayi amfani da wannan damar a fito duniyar social media a dauki nauyinsu da jaridu da rediyo da telebijin a yada, sunyi wannan tsarin domin a tunaninsu ta hakane zasu jefa tsanar gwamnatin shugaba Buhari a cikin zukatan talakawa.
Jam’iyyar PDP maciya amana sun manta cewa Shugaba Buhari a hannun PDP ya karbi yaki da wannan ta’addancin, a gwamnatin PDP aka kyankyashe ta’addanci a Nigeria, duk abinda shugaba Buhari yake yi a yanzu gyara ne na abinda gwamnatin PDP maciya amana suka lalata, kuma kowa ya shaida cewa gwamnatin shugaba Buhari ta karya kashin gadon bayan Boko Haram har suka karkasu, yanzu barazanar ISIS na duniya da ta kawo musu tallafi ta hanyar kasashen Nigeria makwabta ake fuskanta a yankin tabkin chadi, za’a iya cin nasara akansu idan kasashen suka baiwa gwamnatin Buhari hadin kai.
Kuma duk da shugaba Buhari bai halarci jana’izar sojojin da suka rasa rayukansu a harin Metele ba wannan ba shine abin damuwa ba, abinda ya kamata shugaba Buhari yayi shine lalubo hanyar da za’a kawo karshen ‘yan ta’addan, kowa ya gani a daidai lokacin da akayi jana’izar sojojin; shugaba Buhari ya gayyato shugabannin kasashen da ke iyaka da tabkin chadi ya tattauna dasu kan hanyoyin da za’abi a kawo karshen ‘yan ta’addan
Me yasa Atiku Abubakar bai fito ya yabawa wannan matakin da shugaba Buhari ya dauka ba?
Bana mantawa PDP lokacin mulkin Jonathan an tayar da wasu manyan bama-bamai a Abuja mutum kusan dari biyu suka hallaka, amma Jonathan haka ya tsallake suka tafi Kano a ranar suna ta tikar rawa da karuwai babu tausayi babu tsoron Allah a zukatansu, bai kamata ace Atiku Abubakar ya manta da wannan ba.
Don Allah Baba Atiku ku canza salon siyasa, domin kun riga da kun cuci ‘yan Nigeria, kuma masu hankali daga cikin ‘yan Nigeria basu manta da cutar da kukayi ba, hakuri ya kamata ku baiwa ‘yan Nigeria watakila su amince daku su sake baku rikon amana a karo na biyu.
Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka bashi nasara akan ‘yan jari hujja maciya amana macuta.
Post a Comment