MURNAR SAKE LASHE ZABE KO FARIN CIKIN ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA ?
Daga Garba Tela Hadeija
Kamar yadda akasarin jama’a su ke sane, yau ranar Talata, 17 ga watan Disamba, shekarar 2018, Shugaban ‘kasa, babban kwamandan askarawan Nageria, Alhaji, Sir, Muhammadu Buhari, (GCFR), ya cika shekaru saba’in da shida (76) a Duniya.
Tun a jiya da kafin jiyan hadi kuma da yau, na ke nazartar sakonni da wallafe-wallafen al’ummar Nageria, a shafukan yanar gizo-gizo, (Social Media), kuma duk akasarin jama’a, sun karkata ne wajen taya Shugaba Muhammadu Buhari farin ciki da murnar zagayowar wannan rana da aka haife shi ne.
Hakika, a ‘dan abin da na nazarta kan wannan rana, na ‘kara gamsuwa da ‘karuwar yakinin lallai har yau Shugaba Muhammadu Buhari ya na nan ‘damfare cikin zukatan al’ummar Nageria.
Jama’a ba su ‘kosa da shi ba, ba su gajiya da shi ba, har gobe ‘kaunarsa na cikin ruhin al’umma, kuma ba sa fatan rabuwa da shi, sannan a shirye su ke tsaf! Su sake zabarsa a karo na biyu domin ya cigaba da ayyukan alkhairan da ya faro musu.
Duba da yadda ‘kasa ta ‘daukwa ta ko’ina ana ta taya Shugaba Buhari farin ciki da murnar zagayowar wannan rana da aka haife shi, kai ka ce murnar sake lashe zabensa karo na biyu ake yi, domin duk ‘kasa ta rude da shagalin murnar zagayowar wannan rana da aka haifi ‘dan ‘kasa nagari, mai gaskiya, mutumin kirki, (Muhammadu Buhari).
Ba shakka, ko iya mutanen da su ka fito taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar wannan rana, su kadai sun isa kayar da abokan karawarsa a ranar zaben shekarar (2019).
#HappyBirthdayToYouBaba, Allah ya ‘kara lafiya da jinkiri mai albarka, ya kuma iya maka sake samun nasarar lashe zabe a wannan karo na biyu domin cikar burinka na gina sabuwar Nageria a mataki nagaba, #NextLevel, fatan alkhairi Baba.
Post a Comment