Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Assalamu alaikum, Bayan gaisuwa ta addinin da mu ka yi tarayya da Kai. Tare da fatan kana lafiya, a daidai wannan loton, kuma Muna rokon Allah ya Kara maka ita, da kwarin guiwar Jagoranci nagari.

Mai girma shugabanmu kamar yadda ka sani daya daga cikin jiga-jigan dalillan da na sa mu ka zabe ka shi ne; domin Samar da tsaro mai nagarta musamman a yankin arewa maso Gabas da Kungiyar Boko Haram ta daidaita, Wanda ya kusa karade arewa baki daya. Alhamdulillahi cikin Iyawar Allah mu ka yi nasarar kayar da gwamnati Mai ci a lokacin mu ka zabe ka, jahar Zamfara na daya daga cikin jahohin da su ka baka gagaruwamar kuri’a, da ba a taba baiwa wani Dan takarar Shugabancin kasa ba.

Wanda a tunanenmu sakamakon kyautatawa, shi ne kyautatawa ko da a duniyance ne.

Shugaba Buhari tun kafin ka hau mulki Zamfara muna fama da tashin hankali na barayin shanu da ke kisa suna fyade tare da garkuwa da mutane suna amsar kudin fansa tare da kone dukiyoyinmu, musamman a cikin karkara. Sai dai Bayan hawan mulkinka abun ya fi muni matukar gaske, Wanda yanzu an wayi gari ba wani lungu da sako na jahar Zamfara da ba mu fama da wannan matsalar, kullum sai an kashe rayukka, an yi garkuwa da mutane, tare da yiwa mata fyade da mummunan salwantar da dukiyoyinmu da ke faruwa.

Har an wayi gari shanu sun Kare Noma ya gagari al’ummar jahar duk da noman shi ne abun alfaharinmu, Wanda Hakan ya yi sanadiyar jefa rayuwar mu al’ummar jahar Zamfara cikin wani mawuyacin halin da, da dama daga cikinmu ba mu iya ciyar da kanmu abinci sau uku a rana. Manyan garuruwa irin Gusau, duk kwararon da ka shiga da wahala ba ka yi arba da ‘yan gudun Hijira mata da kananan yara suna barace-barace Dan neman abunda za su ci, su rayu a sararin subuhana, ba.

Wanda Kai tsaye ba za mu ce shi Gwamnan jahar ke daukar nauyi da baiwa ‘yan ta’addar makamai suna kisanmu ba. Amma mun tabbatar da rashin daukar mataki da Kula da al’ummarsa na daga cikin manyan dalillan da ya sa kullum matsalar sai karuwa ta ke yi. Mun yarda Gwamnan na kashe, kudi a bangaren tsaron. Amma na banza tunda mu dai talakawan da ke fama da matsalar ba mu ganin alamarsu.

Yanzu haka Maganar nan da na ke yi duk da masifaffen halin da mu ke ciki, Gwamnan jahar Zamfara, baya cikin jahar dama kasar baki daya, Hasalima Wallahi ba mu San gaskiyar Inda ya ke ba zuwa yanzu.

Mai girma Shugaban kasa, daya kuma jigo daga cikin nauyin da ya rataya ga kowane shugaba, shi ne Samar da tsaron rayukka da dukiyoyin al’umma. Kuma duk Gwamnatin da ta kasa haka. To hakika Gwamnatin nan ta kasa. Hakika mun sani cewa Gwamnatinka Tana kokarin Samar da tsaro a kasarmu Najeriya, kuma an samu sauyi matuka a bangaren arewa maso Gabas Inda a baya ‘yan Boko Haram su ka ci karensu babu babbaka, har abun ya kusa karade arewa baki daya dama Najeriya kwata. Amma yanzu ko a arewa maso Gabas din ba ko ina ake samun jefi-jefi na aika-aikar Kungiyar Boko Haram ba. Wanda duk wannan nasarar za mu ta’allaka ta da jajircewar Gwamnatinka.

Sai dai abun mamaki a jahar Zamfara kullum tashin hankali sai karuwa ya ke yi kamar wutar jeji, kuma Kai da mu ke da matukar aminta da cewa Mai kaunar mu talakawa ne. Ka zura Muna Ido ba wani mataki kwakkwara da mu ka ga Gwamnatinka na dauka, Wanda mu ka gani a zahiri. Wanda a shekarar 2016 ka shigo jahar akan matsalar jahar, har ka bar jahar ba wani kwakkaran mataki da mu ka gani a zahiri ka dauka. Hasalima Inda ake hasashen a ga jami’an tsaro a jibge wani wurin ba a ma ko ganin keyarsu.

Haka zalika duk wani yunkuri da za ka ji an yi na Samar da tsaro a jahar Zamfara, daga karshe sai dai ya koma labarin kanzon kurege Wanda ba wani takamammen aikin tsaron da al’ummar karkara su ke gani.

Dan haka mai girma Shugaban kasa, hakika Allah ya baka dama da iko tare da sanya sonka a cikin zuciyarmu da ya sa mu ka Zabe ka, kuma kullum Muna cigaba da yi maka addu’a da ita Kanta gwamnantin taka addu’ar samun nasara Marar misaltuwa. Sai dai kash! Maganar gaskiya mu al’ummar jahar Zamfara, Tuni da dama daga cikinmu mu dawo daga rakkiyarka, domin Muna daukar, cewa Kai da Gwamnatinka kun mayar da mu saniyar ware ne, kwata-kwata ba ruwanka da abunda ke faruwa a jahar Zamfara. Wanda ka zura Ido, Gwamnanmu na wasa da rayukkkanmu. Wanda na tabbatar da kana yiwa Gwamnanmu Maganar ya dena yawace-yawacen banza da yofin da ya ke yi, na ba gaira ba Dalila ya tsaya cikin jaharsa ya rungume su, duk matsalar tsaron da ake fuskanta ya Kai dauki Inda abun ya fi karfinsa ya Sanar da Kai, da ba za a wayi gari, ana kisanmu kullum shi ko a jikinsa ba. Wanda Asalima yanzu da na ke wannan rubutun Allah dai ya San kasar da ya ke. Ba daukar wani matakin kirki Maganar jaje bata taso ba uwa uba tallafi.

Dan haka Muna Kira ga Gwamnatinka Mai adalci ta dubi yuyuwar daukar matakin da ya dace, domin magance wannan matsalar. Domin Wallahi mu dai al’ummar jahar Zamfara ba mu san amfanin mulkinka ta bangaren tsaro ba, har ma wani loton mu kan ce, mu dai a jahar Zamfara gwamma LOKACIN mulkin PDP da naka mulkin, dan lokacin mu ba mu San wani tashin hankali kamar wannan ba.

Daga karshe Muna rokon Allah ya sa wannan koken namu ya Kai ga kunnuwan da mu ka yi koken dan su, ya kuma ba su ikon share muna hawayen jinin da ke kwarara a idanunmu.

Allah muna rokonka ka baiwa jajirtattun jami’an tsaron mu ikon tarwatsa gungun makiyan zaman lafiya a duk Inda su ke

Allah mun tuba, ka yafe Muna, ka kawo Muna zaman lafiya dauwamme a jaharmu ta Zamfara da Nijeriya baki daya.

Post a Comment

 
Top