SIRRIN ZAMAN DA SU ATIKU ABUBAKAR SUKAYI A KASAR DUBAI YA FALLASU

Daga Datti Assalafiy

Babban Maigidana Masoyina Dr. Idris Ahmed bakin fata na farko a tarihin duniya da ya mallaki karatun digiri na uku (Phd) a “Cryptology”, wadanda suke tare dashi a wannan dandali na facebook idan baku manta ba kafin BBC ta hada baki da maciya amanar Nigeria su kai karansa zuwa kamfanin facebook a kulle masa asalin facebook account dinsa, Dr Idris Ahmed ya wallafa wani labari da yace su Atiku Abubakar sunyi zama a kasar Dubai sukasa aka nemo musu kwararrun ‘yan dandatsar na’ura mai kwakwalwa (Computer Hackers) suka basu kwangila akan yadda za’a yiwa na’urorin hukumar zabe na kasar Nigeria (INEC) kutse domin su samu damar canza sakamakon zabe

Bayan Dr. Idris Ahmed ya wallafa labarin to a daidai lokacin ne BBC tayi karan shafinsa na facebook aka kulle, sai suka tura masa da sako ta email dinsa cewa an kulle masa shafin ne saboda ya kwatanta kabilar berom a matsayin ‘yan ta’adda masu cin naman mutane, wai wannan shine laifinsa

Yau an wayi gari jam’iyyar APC ta fito ta tabbatar da abinda Dr Idris Ahmed ya wallafa tun kafin su Atiku Abubakar su dawo daga zaman sirrin da sukayi a Kasar Dubai

Mataimakin sakataren yada labarai na ‘kasa a jam’iyyar APC Yakini Nabena ya fito a hukumance ya sanar da duniya cewa sun gano boyayyen shirin da jam’iyyar PDP tayi a zaman da jagororinta sukayi a kasar Duba, inda suka nemo wasu kwararrun ‘yan dandatsar na’ura mai kwakwalwa daga ‘kasar Rasha (Russia) suka basu kwangilar yiwa manyan na’urorin hukumar zabe na ‘kasar Nigeria kutse da dandatsa domin a canza bayananta

Cikin wadanda akayi zaman sirrin dasu a Dubai akwai ‘dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar maciya amana (PDP) Atiku Abubakar, shugaban jam’iyyar PDP na ‘kasa Uche Secondus, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da da sauran wasu shugabanni a jam’iyyar ta maciya amana PDP

Yakini Nabena ya kara da cewa tsarin dokar hukumar zaben Nigeria da ake amfani dashi yanzu a Nigeria PDP ce ta tsara, su suka kirkira amma yanzu su suke tsoron tsarin saboda babu kofar magudi, don haka abinda PDP takeyi yanzu na sukar tsarin dokokin zaben Nigeria yana daya daga cikin ajandar zaman sirri da sukayi a kasar Dubai

Duk abinda PDP takeyi yana cikin ajandar da sukayi a Dubai, da farko sun fara da haddasa yajin aiki na ma’aikatan Nigeria domin su haddasa matsala a cikin kasa amma basuci nasara ba, sun haddasa yajin aiki na jami’o’in gwamnatin Nigeria, yanzu kuma suna kokarin haifar da karancin man fetur a fadin tarayyar Nigeria, wannan duka yana daga cikin ajandar zaman sirri da su Atiku Abubakar sukayi domin su cimma mummunan burinsu na siyasa

Babban ajandarsu yanzu shine batun canza dokar hukumar zabe na ‘kasa, mummunan kudurinsu shine idan shugaba Buhari yaki ya saka hannu a sabon dokar zabe na ‘kasa da su sanata Bukola Saraki suka canza shine sai su fito yin zanga-zanga, Yakini Nabena yace muna jiransu su fito zanga zangar, tayaya PDP zasu canza dokar zabe na ‘kasa suce wai da zaran an kada kuri’u a saka bayanan a nu’ara ba tare da an kirga kuri’un a bainar jama’a ba?, to wannan yana daga cikin ajandar da suka tsara a kasar Dubai, shiyasa shugaba Buhari yaki saka hannu a sabon dokar zaben da fadar majalisan dattawa karkashin jagorancin Bukola Saraki suka canza

Sun baiwa kwararrun ‘yan dandatsar na’ura mai kwakwalwa ‘yan asalin ‘kasar Dubai kwangila ta yanda shugaba Buhari yana saka hannu a sabon dokar hukumar zabe na ‘kasa da su Bukola Saraki suka canza to zasu shigo da wadannan ‘yan dandatsar na’ura mai kwalkwalwa cikin Nigeria domin su aiwatar da kwangilar da suka basu

Jama’a kunji abinda PDP maciya amana suka tsara zasu aiwatar domin su kwaci mulkin Nigeria ta hanyar ha’inci da cuta da magudi, kuma abune mai yiwuwa ayiwa manyan na’urorin zabe na ‘kasa kutse da dandatsa, hatta gwamnatin Amurka sai da ta fuskanci matsalar kutse a na’urorin zaben ‘kasar domin a canza bayanai, balle kuma ‘kasa irin tamu Nigeria

Ya kamata ‘yan Nigeria mu saka wannan mummunan ajanda na PDP a cikin addu’ah, kamar yadda suke kokarin yin kutse da dandatsa a abinda yake ‘yanci ne da hakkin ‘yan Nigeria, to muyi fatan Allah Ya shiryesu, idan ba zasu shiryu ba Allah Ya dandatsasu Ya kare al’ummar Nigeria daga sharrinsu Amin

Post a Comment

 
Top