Daga Bello Muhammad Sharada

Dokar kasafin kudi wato a Turance Appropriation Law ko Budget Law ita tafi kowacce doka muhimmanci a sha’anin gudanar da mulkin kasa. Ita ce dokar da take raba yadda za a samu kudi ta kowacce fuska da kuma yadda za a raba su da kashe su a duk fadin kasa.

Idan jami’an gwamnati wato ministoci da manyan sakatarori da shugabbannin hukumomi suka tsarawa shugaban kasa kasafi, tsarin mulkinmu ya wajabta masa ya gurfana a gaban ‘yan majalisu na tarayya su 360 da na dattijai su 109 ya gabatar da wannan kasafin.

In ya gabatar ya tafi, su kuma ‘ya majalisa zasu rika kiran ma’aikatu da jami’ansu daya bayan daya suna tsefe abin da shugaban kasa ya gabatar, suna kari suna ragi, su gyara nan su soke can, har a samu daidaito. In an samu cimma matsaya, sai majalisa ta mayar wa da shugaban kasa wannan kiyasi, shi kuma ya sanya masa hannu. Duk abin da za a yi na tafiyar da kasa za a gabatar da shi a doron wannan kasafi. Laifi ne babba a ki amfani da dokar in an sanya mata hannu, tana iya kaiwa ga tsige shugaban kasa

Tunda aka dawo mulkin farar hula a wannan jamhuriyya daga shekarar 1999 har zuwa shekara ta 2015, in banda dan lokacin da marigayi Ummaru Musa Yar Adua ya yi shugabanci, kasafin kudi aikin banza ne, za a rubuta, za a tsara, za a karanta, za a maida shi doka, amma ba za a yi aiki da shi ba.

Da ministoci da manyan ma’aikata da shugabannin hukumomi da suka fahimci dokar kasafi ta zama karya kawai, sai kawai basa maida hankali a wajen ingantata, duk shekara basa sauya komai. Misali in sun ware wa harkar wutar lantarki naira dubu daya a shekarar 2000 idan shekara ta zagayo ta 2001 sai su kara dubu daya kawai akan kasafin bara, an wuce gurin. In kaga an bi tsari to fa wani gagarumin aiki ne kuma zai hada da bashi ko da wata yarjejeniya da wasu mutanen kasar waje ko kamfanoni masu zaman kansu ko dai masu mu’amilla ta gaske ba siyasa.

Suma da ‘yan majalisa suka gane haka, sai su rika hada baki da ma’aikatansu na majalisa da ma’aikatan gwamnati suna cusa karya da harambe a kasafin, suna janye kudaden ta wata hanyar don rashin gaskiya. Wannan ita ce a’aldar da aka saba.

Kwatsam sai guguwar canji ta taso ta APC. Mutanen kasar nan sun zabi Muhammadu Buhari da sa rai zai dake ya sauya abubuwa da tunani iri-iri, zai zo da fasali sabo kar, kuma zai gina ginshiki da za a ci gaba da amfani da shi don ceton Najeriya.

Wannan majalisar ta takwas ta hada Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, a cikinta akwai kabilar kowanne yanki na kasar nan, da jam’iyyu akalla guda shida, da wakilai da suka zo daga mabanbantan ra’ayi da tunani. Mu’amala da su sai an nuna siyasa da diflomasoyya da dabaru da cizawa da hurawa da hadin kai.

A cikin littafin da ya rubuta na tarihinsa Beckoned to Serve, Alhaji Shehu Shagari, ya yi bayanin irin yadda ake mu’amala da ‘yan majalisa a tsarin Presidential System, yana cewa kusancin da yake da shi da ‘yan majalisa ya kai ga ya san suna da lambar wayar kowane dan majalisar tarayya da dattijai wanda yake da mukami daga kowacce jam’iyya, kuma yana magana da su kai tsaye a duk lokacin da wata mas’alar kasa ta taso.’Yan majalisa basu da shamaki suna hulda shi ta sanayya sosai.

Shima Lee Kwen Yu, tsohon shugaban kasar Singapore wanda yake abin alfahari a gurinsu, a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna From Third World To First ya yi bayanin cewa ya san duk ‘yan majalisar kasarsa da yanayinsu, kuma sam baya wasa ko kadan da irin bukatun da suke zuwa da su saboda sune abokansa na aiki.

Na duba littafan tarihin siyasar kasar da yawa tun daga kan shugabanni da suka jagoranci nemarwa kasar nan ‘yancin kai, har zubin farko na ‘yan siyasa a kudu da arewa, ina nufin su Sardauna da Aminu Kano da Tafawa Balewa da Awolowo da Azikwe da wadanda suka biyo bayansu su Shehu Shagari babu wanda ya samu soyayya da maitar kauna kamar Buhari.

Abin mamaki kuma babu wanda cikin kankanin lokaci ya samu zubewar kima da daraja daga masoya da wadanda suke binsa a siyasa kamar Buhari. A lokacin da Buhari zai gabatar da kasafinsa na farko wato na shekarar 2016, ‘yan majalisa da duk ‘yan Najeriya suna cikin zumudi da Allah-Allah kuma a shirye suke su yi duk abin da yake so.

Amma ina! A kasafin karshen zangonsa na farko, sai ga shi ana yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu, ana hana shi magana, ana gaya masa karya yake yi a lokacin da yake karatu. Masu wannan ihun ‘yan jam’iyyarsa ne da ‘yan hamayya, a zauren majalisa a gaban duniya.

ME YA JAWO HAKA? Insha Allahu zan bada amsa.

Post a Comment

 
Top