Ba Sai Ka Zo Yakin Neman Zabe Wajenmu Ba, Sakon Mutanen Misau Ga Gwamnan Bauchi

…ayyukan da ka yi mana sun gamsar da mu!

Daga Mashkur Ibrahim

Hausawa na fadin gani ya kori ji, shin wane abu kake dashi da zaka nuna kayi alfahari da Gwamnatin jihar ku?

Su dai Al’ummar Misau da Udubo zuwa Gamawa suna da abun nunawa.

Wannan hoto da kuke gani hoton hanya ce da Gwamnatin jihar Bauchi a karkashin Barista M.A ya shimfida masu wacce ta tashi tun daga Misau ta ratsa ta Udubo ta bulle zuwa Gamawa.

Hanyar wacce ta kai kilomita 100 jama’a suna alfahari da ita saboda alfanun da hanyar take dashi wajen hada-hadar kasuwanci a jihar musamman ga mazauna yankin da ma jihar baki daya.

Hausa Times ta ji ra’ayoyin mazauna yankin kamar haka:

Abudllahi Mai Kemis yace “Allah ya gani munji dadin wannan aiki da mai girma M.A yayi mana. Amma dai muna bukatar kari”

Dauda Khamis yace “Ni babban dan adawar Gwamna ne amma hakan ba zai hana ni fadin gaskiya ba, aikin wannan hanya yayi daidai domin tasirin ta a wajen mu”

Naja’atu Nura tace “Kafin ayi wannan hanyar mun wahala amma zuwan M.A ya share mana hawaye. Ni lokacinda aka bayar da labarin za’ayi hanyar duk mun zaci yaudara ce irin ta yan siyasa har sai da muka ga zahiri anyi ta”

KO SHIKENAN IYA ROMON DIMKORADIYYAR DA AL’UMMAR WANNAN YANKI ZASU SHA?

Wakilinmu ta ji ta bakin mai taimakawa Gwamnan jihar Bauchi a fannin sadarwa, Shamsudeen Lukman a inda yace:

“A’a ba shikenan ba, wannan so soman tabi ne ayyuka daban daban suna nan ana yi. Al’ummar jihar Bauchi zasu cigaba da shan romon dimokaradiyya in sha Allah mu dai cigaba da hakuri da taya kasarmu da jihar mu da addu’a”

Muna kira ga mai girma Gwamna da ba sai yazo wajajenmu yakin neman zabe ba, aikin alkhairi da yayi mana ya wadatar damu. Kalli dai wannan titi abun sha’awa!

Post a Comment

 
Top