Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Tarihin Sarauniya Abla Pokou, tafe yake hannu da hannu da zamanin da aka ‘kirkiri ‘kabilar (Baoule) da ke ‘kasar Kwaddi Buwa, sannan ya na tuna hannun uwa a lardin wannan ‘kasa da kuma ‘daukacin ‘kabilar (Akan).

An haifi Sarauniya (Abla Pokou) a cikin gidan sarautar Ashanti da ke ‘kasar Ghana, sannan ‘yar ‘dan uwan babban basarake ce (Osei Tutu), ma’assasin daular Ashanti. Saboda al’adar Ashanti kan gado, lokacin da Sarki (Osei Tutu) ya mutu, sai (Dakon) ‘dan uwan (Abla Pokou) ya gaji sarautar, amma sai aka samu sabani kan yarjejeniya tayadda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar (Dakon).

Sarauniyar sai ta ji tsoron rayuwarta, nan da nan ta yanke shawarar su gudu daga masarautar zuwa kotunta. Bayan shafe doguwar tafiyar kwanaki sai su ka samu nasarar isa gabar kogi (Camoe River), wanda ya ke tsakanin iyakar Ghana da Kwaddi Buwa, kamar yadda aka sani, wannan kogi, kogi ne mai matukar hatsari, amma haka su ka tunkari ratsa shi cikin karfin gwiwar su tsallake ko kuma su fuskanci mutuwa.

To, yanzu kuma labarin ya fara, inda sarauniyar ta dubi allon dubanta, ta tambaye shi ko shin me za su sadaukar domin hanya ta bude musu, sai ya amsa mata da cewa, dole sai sun sadaukar da abin da ya fi soyuwa a gare su.

Da jin haka, sai duk matan kotun har da Sarauniyar su ka cicciro kayan adonsu domin sadaukar da su, maza kuma sai su ka sadaukar da dabbobinsu, amma kuma sai abin duban ya dakatar da su tare sa yi musu ishara da yayansu a matsayin abu mafi soyuwa a gare su. Daga ‘karshe sai sarauniya ta janyo ‘danta daga bayanta tare da fadin “Kouakou, ‘dana ne ‘daya tilo ka yafe mun, domin na fahimci akwai bukatar in jefa ka cikin wannan kogi domin ceton al’ummata, duk yawan mata ko uwa, sarauniya Sarauniya ce”.

Sannan ta jefa shi cikin kogin a matsayin sadaukarwa domin ceton al’ummarta da kuma ‘dorewar sarautarta. Sai ta jiyo kukan ‘danta daga cikin wannan kogi ya na fadin “Ba ouli”, ma’ana ya mutu ga al’ummarta nan, sannan sai hanya ta bude tare da ba wa sarauniya da al’ummarta damar tsallakawa.

Wasu kuma su ka ce wata ‘katuwar bishiya ce ta tare musu hanyar, wasu kuma su ka ce a’a. Bayan da su ka tsallaka kogin lafiya, (Pokou) da al’ummarta sun zauna a ‘kasa da ke tsakanin Kogin Camoe da Bandama.

Bayan da su ka zauna, sai ‘kabilar ta gabatar da jana’izar yaron da aka sadaukar, kuma ana tuna wurin tare da kiran wurin da su na (Sakassou), ma’ana, wurin jana’iza.

Sarauniya (Pokou) ta mulki dumbin al’ummarta tsawon shekaru masu yawa, sannan labarin kykkyawan zamaninta ya isa wurare masu nisa. Ta mutu wajajen shekarar alif da ‘dari bakwai da sittin (1760).

A yau ‘kabilar (Baoule), al’umma ce mai matukar yawa a Kwaddi Buwa, sun shafe ‘kananan ‘kabilu tun zamani mai tsawo da ya shude. Wadannan Hotuna da ke ‘kasa, mutum-mutumi ne na (Kple Kple) ‘yan rawa a ‘kauyen (Baoule) a ‘kasar Kwaddi Buwa.

Post a Comment

 
Top